Mafi kyawun Abinci da ya kamata mai gyambon ciki watto Ulcer ya ci

0
723

 

Gyambon ciki shine buɗaɗɗen raunuka waɗanda ke tasowa akan rufin ciki.  Hakanan ana iya kiransu da gastric ulcer ko peptic ulcer a turance. Wannan Cutar na iya shafar mutane tun suna ƙanana, amma sun fi yawa a cikin mutane sama da shekaru 60.  Maza kuma sun fi samun matsalar gyambon ciki.

Ulcers na faruwa ne lokacin da acid daga abinci mai narkewa ya lalata bangon ciki.  Mafi yawan abin da ke haifar da gyambon ciki shine kamuwa da cuta daga kwayoyin cuta mai suna HELICOBACTER PYLORI.  Na dogon lokaci mutane sun yi imanin cewa gyambon ciki na faruwa ne ta hanyar wasu zaɓin salon rayuwa.  Mutane da yawa sun yi tunanin cewa cin abinci mai yaji da fuskantar damuwa suna da alaƙa da ulcer, amma babu wata kwakkwarar hujja da ta tabbatar da waɗannan abubuwan.

Gyambon ciki na iya buƙatar salon rayuwa da canje-canjen abinci don sarrafa su yayin da suke warkewa.  Magungunan rage acid na iya zama da amfani.  Kamar yadda Akwai abinci da ya kamata mai gyambon ciki ya kaurace wa haka zalika Akwai Mafi kyawun abincin da ya kamata ku ci idan kuma da gyambon ciki sun haɗa da:

 Abincin Mai dauke da Fiber

Wannan ya hada da Alkama, hatsi,  tsaba, gyada, lemu, tufa da karas.  Wadannan abinci suna da amfani a gare ku saboda suna iya taimakawa wajen hana gyambon ciki  tasowa.

Abincin Mai dauke da bitamin A

Abinci kamar dankali Hausa, ganyen Kale, alayyahu na dauke da Vitamin A. Wadannan abinci na kara samar da gamsai a cikin hanjin, wanda wasu ke ganin zai iya taimakawa wajen hana gyambon ciki.

 Koren shayi

Binciken da ya fito ya nuna cewa koren shayi na iya taimakawa wajen yakar helikobacter pylori.wadda hakan ke nufin yana da kyau masu gyambon ciki  su yawaita sha.

Daga: Firdausi Musa Dantsoho