RIKICIN APC,AN NADA GWAMNA ABUBAKAR SANI BELLO A MATSAYIN SHUGABAN JAMM’IYAR APC TA KASA

0
66

A dai dai lokacin da ake rade-radin cewa,Shugaba Muhammadu Buhari ya tuge Mai Mala Buni a matsayin shugaban fati na APC inda aka nada Gwamnar Neja Abubakar Sani Bello a matsayin mai rikon kwarya.

Bello ya bayyana matsayin sa,a lokacin da ya jagoranci rantsar da shugabannin Jamm’iyar na jihohi a Abuja ranar litinin bakwai ga watan maris 2022.

A cewar sa, ya kama aikin ne a sanadiyar tafiya da Buni ya yi.Ko da yake a baya bayan nan,an yi hasashen cewa zai karbi mulki a hannun Mala.

Shugaban rikon kwaryar ya kara da cewa,shugannin jihohin sun yi rantsuwar kama aiki a yau,kuma mun tattauna ci gaban da aka samu kan yarjejeniyar da kuma abinda ya kamata ayi na gaba domin cimma burin mu na 26 ga watan maris.

Daga Fatima Abubakar.