Mahaifiyar fitaccen malamin addinin musulunci Sheikh Ahmad Abubakar Gumi ta rasu.

0
27

Mahaifiyar fitaccen malamin addinin musulunci Sheikh Ahmad Abubakar Gumi, ta rasu.

Sheikh Ahmad Gumi ya sanar cewa mahaifiyar tasa ta rasu ne a wani Asibiti da ke garin Abuja da misalin karfe 5:30 na yammacin ranar Lahadi.

Sheikh Gumi ya wallafa a shafin sa na yanar gizo cewa;

“Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun. Yau ina cikin alhinin ina sanar da rasuwar mahaifiyata…; Don Allah a roka mata gafara da rahamar Allah.

“Maganar karshe da ta yi min makonni uku da suka wuce ita ce, ‘in sha’a Allahu, Allah Zai sada ta da ’ya’yanta da jikokinta a Aljannah’.

“Wadannan kalaman sun kara min kwarin gwiwa; Allah Ya kai rahamarsa gare ki. Amin,” kamar yadda ya wallafa.

Malamin ya sanar cewar za a yi jana’izarta da misalin karfe 1 na rana a ranar Litinin bayan Sallar Azahar a gidan marigayi Sheikh Abubakar Mahmud Gumi da ke Unguwar Sarki GRA, bayan Lugard Hall, Kaduna.

 

Daga  Fatima Abubakar.