MAI TSARON GIDA A GASAR WASAN CIN KOFIN AFRIKA YA DAWO FAGEN DAAGA,BAYAN WARKEWA DAGA RAUNI.

0
56
Babban kungiyar kwallon kafa ta kasa Nijeriya wato super eagles na ci gaba da burgewa a kasar Kamaru a matsayin daya daga cikin manyan ‘yan wasanta na baya,mai tsaron gida Wanda bai buga gasar cin kofin nahiyar Afirkan  ba saboda matsalar motsa jiki, ya murmure.
Dan wasan baya na kungiyar Super Eagles Leon Balogun ya bayyana jin dadinsa na komawa taka leda bayan da aka yi masa jinya.  Balogun dai bai buga wa kulob ko wata kasa wasa ba tun bayan da ya yi rauni a lokacin da Rangers ta sha kashi a hannun Hibs a wasan kusa da na karshe na gasar cin kofin Premier a watan Nuwamba saboda rauni a baya.
  Mai tsaron gidan wanda aka haifa a Berlin yana daya daga cikin mutane 28 da aka ware da za su buga wa Nijeriyan  gasar ta Afcon.
A shafinsa na twitter Balogun ya shaidawa mabiyan sa ,farin cikin sa na sake dawowa fagen daaga.