A AWA 48 KACAL NE AKA SACE YAR SHEKARA 8 DA AKAYI GARKUWA DA ITA A ZARIA,JIHAR KADUNA.

0
27

Masu garkuwa da mutane sun kashe wata ‘yar shekara 8, Asma’u bayan karbar sama da naira miliyan 3 kudin fansa a Zariya kwanaki 42 da sace ta.
Lamarin ya faru ne sa’o’i 48 bayan sace wata ‘yar shekara biyar Hanifa A Abubakar da malaminta ya saka mata guba a Kano.
mahaifin Asma’un Alhaji shuaibu ya bayyana yadda aka sace ta ga manema labarai a Zariya. Ya ce: “An sace ‘yata ne a ranar 9 ga watan Disamba a lokacin da ta kasa komawa gida, na kai kara ga ‘yan sanda.
Bayan wasu kwanaki sai ‘yan fashin suka fara kiran lambata, suka bukaci in bada miliyan 15, amma mun yi sulhu, na fara ba su miliyan 2, suka karbi kudin a unguwar Rigasa da ke Kaduna.
Daga baya, sai suka sake kirana suka bukaci in basu wani miliyan daya da dubu dari hudu da hamsin a matsayin kawai sharadin sakin ‘yata. ban yi gardama ba. Amma na ba su kuɗin, Sai dai bayan biyan kudin fansa kamar yadda aka nema a ranar 19 ga watan Janairu, sai suka kira ni suka shaida min sun kashe ta,kuma nan take suka kashe wayar su.
Abin da nake gudu kenan,gashi ya tabbata ,na yi imanin cewa wayanda suka dauke ta makusantan mu ne a unguwa don ina da shaida akan hakan.Na gabatar da shaidan ga yan sanda kuma a halin yanzu an cafke wa’yanda ake tuhuma.
A cewar sa mai magana da yawun yan sanda na ASP Muhammad Jagile,ya tabbatar da aukuwan lamarin,kuma ya ce,hukumar ta yan sanda na kan bincike akan lamarin.
Ya kara da cewa ba zai iya karar da kama wa’yan da ake tuhuman ba,sai ya kira reshen su na Zaria Don karin bayani,daga baya na sanar wa manema labarai.

By Fatima Abubakar.