YADDA ZAMU GYARA JIKINMU DA MADARA DA LEMON TSAMI

0
275

Gyaran jiki akoda yaushe abune mafi muhimmanci musamman ga mata, duk yadda kika kai ga tsafta in har baki gyara jiki toh abu ne da zaiyi saurin nunawa a jikinki. Hausawa sukance in har kinada kyau toh ki kara da wanka.

Shi dai hadin gyaran jiki da mada da kuma lemon tsami yana karawa jiki kyau da kuma haske musamman idan anayi akai akai. Ga bayani kan yadda ake hadin kamar haka:

Zaki samu madaranki na gari sai ki jika kadan da ruwa sannan sai ki matse lemon tsami a ciki. Sai a gauraya sosai sannan sai ki shafe fuska da sauran wuraren da kike bukatan haskensu a jikinki. shi wannan hadin idan ana yinshi akai akai za’aga yadda jiki zai yi kyau, yayi laushi, da kuma santsi. Haka zalika bayan kin shafa sai ki barshi na tsawon minti biyar sannan sai ki wankeshi da ruwan dumi.

Idan har akayi akaga ya fara kawo wani matsala wa fata toh za’a iya dakatawa a tuntubi likita, idan har kuma kin kasance kinyi sau biyu ne bakiga wani canji bat oh in kika ci gaba na tsawon makonni da yardarm ubangiji zaki ga canji.

UMMU KHULTHUM ABDULKADIR.