Ministan babban birnin tarrayya ya kamu da cutan korona

0
59
Ministan Babban Birnin Tarayya, Malam Muhammad Musa Bello, ya sanar da cewa ya kamu da cutar ta COVID-19.
 Bello ya bayyana hakan ne a wani sako da ya wallafa a shafin Facebook ranar Juma’a.
 A cewar Ministan, “anyi Mun gwaji kuma Ina ɗauke da COVID-19.
 “Bayan buya da kare Kai na Daga Cutar covid19 na tsawon watanni 21 (shekara 1 da watanni 9) , kwayar cutar ta kama ni a cikin ƙarshen kwanakin shekara na 2021. Bayan nayi rashin lafiya daga ranar 28 ga Disamba, na yanke shawarar yin Gwajin COVID-19 a safiyar jiya.
 “Sakamakon ya fito a safiyar yau kuma ina ɗauke da Cutar koron. A halin yanzu ina tare da wasu ciwon makogwaro, zazzabi mai zafi da kuma mura. Ina Shan magani kuma na kebe Kai na a gida.
 “Ina jinjina tare da yi wa daukacin ma’aikatan lafiya na birnin tarrayya FCT da sauran wadanda ke kan gaba wajen yakar wannan annoba barka da sabuwar shekara ta 2022. Ina yi mana addu’ar samun sauki cikin gaggawa ga daukacin mu da ke fama da cutar COVID-19.
Masana sun sanar da ni cewa rashin lafiya ta baiyi tsanani ba saboda na dauki allurar rigakafin COVID-19 guda biyu. Ina kira ga duk wadanda ba a yi musu allurar rigakafin COVID-19 da su yi hakan ba.