Allah ya yiwa hadimin Gwamnan Nasarawa Rasuwa

0
9

Allah ya yiwa mai ba Gwamna Abdullahi Sule na jihar Nasarawa shawara kan ayyuka na musamman, Alhaji Murtala Lamus, rasuwa a ranar Talata, 25 ga watan Oktoba. Babban sakataren labaran Gwamna Sule, Ibrahim Addra ne ya tabbatar da rasuwan Lamus a cikin wata sanarwa da ya fitar
Sanarwar ta bayyana cewa kafin mutuwar Lamus, ya kasance babban dan siyasa wanda ke dauke da soyayyar jihar Nasarawa da al’umma a zuciya.
Gwamna Sule ya nuna kaduwa da samun labarin mutuwar hadimin nasa.
Gwamnan na Nasarawa wanda ya sallaci gawar marigayin ya je har makabarta inda aka sada shi da gidansa na gaskiya,
Ya roki Allah ya ji kan marigayi Lamus yasa ya huta sannan ya baiwa yan uwa da abokansa juriyar wannan rashi da suka yi.
Daga Faiza A.gabdo