Rahama Sadau Za Ta Yi Fim Din Bollywood A Karon Farko Bayan An dakatar da ita A Kannywood

0
290

Jarumar fina -finan kasar Najeriya, Rahama Sadau, na shirin fara fitowa a masana’antar fina -finan Indiya na Bollywood.

Sadau, a ranar Alhamis daya gabata, ta wallafa hotuna daga cikin shirin fim mai taken ‘Khuda Haafiz 2’.

A cikin hotunan da ta wallafa a shafinta na Twitter, an ga jarumar ‘yar asalin jihar Kaduna tare da wasu’ yan wasan Indiya, ciki har da Vidyut Jammwal, babban jarumin fim din Khuda Haafiz.

Ta kuma wallafa hotunan a kan shafin nata na Instagramhandle tare da wallafa rubuta da harshen turanci muka kuma fasara shi da Hausa kamar haka : “hello Bollywood. . . “Munan tare da Vidyut Jammwal Vidyut Jamwalions ‘ #KhudaHafeezChapter2 #Day31 #Bollywood #Lucknow #India #Actors.”

A watan Nuwambar 2020, ‘ kungiyar yan fim na arewa sun dakatar da shahararriyar jarumar a karkashin kungiyar Motion Picture Practitioners Association of Nigeria (MOPPAN), kan wani hotuna da ta wallafa a kafafen sada zumunta.

Kungiyar ta ce hoton da jarumar ta fitar ya haifar da kalaman batanci ga Manzon Allah.

A baya dai, kungiyar masu shirya fina -finan arewa ta dakatar da jarumar a watan Oktoban shekarar 2016 saboda irin wannan abubuwan.

Duk da haka, hukumar tace fina -finai ta jihar Kano tayi mata afuwa ba tare da wani sharadi ba a shekarar 2018.

 By: Firdausi Musa Dantsoho

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here