Jarumar fina-finan Kannywood, Hadiza Gabon, ta shaida wa wata kotun shari’a da ke zamanta a Kaduna cewa rayuwarta na cikin hadari.
Wani ma’aikacin gwamnati mai suna Bala Musa ne ya kai ta kotu bisa zargin kin aurensa bayan ya kashe mata kudi 396,000.
Jarumar dai a zaman da ta gabata ta musanta cewa ta san mai korafin.
Alkalin kotun ya dage sauraron karar daga ranar 28 ga watan Yuni, 2020, biyo bayan rashin lafiyar matarsa zuwa ranar 1 ga watan Agusta domin mai karar ya gabatar da shaidarsa.
Da take jawabi a kotun, wadda ake zargin ta bakin lauyanta, Barista Mubarak Sani Jibril, ta ce da tabarbarewar tsaro a kasar, jarumar tana tsoron kare lafiyarta.
A cewarsa, suna cikin damuwa a kullum shari’ar ta taso a kotu domin ita (Gabon) ta kan fita daga kotun ne a boye.
“Tsaro na yana da mahimmanci, tsaronta yana da mahimmanci, haka ma tsaron sauran mutane yana da mahimmanci a cikin kotu har da na mai korafi.
“Raina na cikin hadari, rayuwarta na cikin hadari, ita ma rayuwar mai korafin na cikin hadari. Ba za mu san wanda ke ganin lamarin a shafukan sada zumunta ba. Abu na gaba za ku fara ganin mutane da bindigogi a nan don yin garkuwa da su. Wannan shi ne abin da ke damunmu ba shari’ar da ake yi a kotu ba,” inji shi.
Lauyan ya kuma yi kira ga kotun da ta duba lafiyar wanda yake karewa ta hanyar amincewa da rashin halartar zaman kotun.
A nasa martani, Lauyan mai kara, Barista Naira Murtala, ya yi watsi da rokon da aka yi mata na kada ta halarci zaman kotun, inda ya ce dole ne wanda ake tuhuma ya kasance a gaban kotu.
Dangane da kare lafiyar wanda ake tuhuma da kuma wanda ya kai karar, ya ce watakila ba zai ki amincewa da bukatarsu kan lafiyar wanda ake tuhuma ba saboda kasar ba ta da lafiya ga kowa amma suna bukatar a rubuta shi a rubuce domin ya yi karatu.
Alkalin kotun, Khadi Rilwanu Kyaudai, ya ba su tabbacin cewa kotun za ta duba lafiyar bangarorin biyu a zaman na gaba.
Fatima Abubakar