Rikicin Malam Ali na Kwana casa’in da hukumar tace Fina finan ta san ya shi ficewa daga kannywood.

0
61

To saidai abin tambaya anan shine meyasa hukumar ke tuhumar sa ? Shin akan tsohun laifin da ya aikatawa hukumar a bayane ?Ga cikakken al amarin dai👇

Daga yau na fice daga Kannywood – Malam Ali na Kwana chasa’i.

Mallam Ali na kwana casa’in ya fice daga kannywood, shin ko waye zai maye gurbinsa acikin kwana casa’in?

Jarumi Sahir Abdul, Malam Ali na shirin Kwana Casa’in ya bayyana ficewarsa daga masana’antar Kannywood.

Jarumin Wanda yayi shuhura a social media ya bayyana ficewar tasa ne ranar Alhamis 30-05-2024 jim kada bayan Shugaban Hukumar Tace Finafinai ta Jihar Kano, Abba El-Mustapha, ya jaddada cewa ba za su yi masa afuwa ba.

Jarumin ya nemi afuwar duk wadanda ya bata wa rai a baya kamar yadda tashar Freedom Radio ta rawaito

Idan zaku iya tunawa hukumar tace fina-finai da dab’i ta jihar kano karkashin jagorancin Abba El-mustapha ta dakatar dashi daga shiga fina-finan hausa tsawon shekaru 2, sakamakon wani bidiyo da jarumin ya saka, wanda hukumar ke ganin ya sabawa doka da tarbiyyar jihar kano.

Hukumar ta zargi jarumin da aka fi sani da Malam Ali a shirin Kwana Casain da wallafa bidiyo mai dauke da batsa.

Sai dai shiyace babu batsa a bidiyo face kalaman hikima da fadakarwa.

Sai dai mutane ma sun ce bidiyon da ya jawowa ‘dan wasan matsala bai dauke da batsa kamar yadda hukumar tace fina-finan Kano ta ke zargi. Da alama watsi da gayyatar da aka yi masa ya jefa sa a matsala. A wani bayaninsa a tashar Freedom, Saheer ya musanya laifin da aka jefa masa.

To sai dai a wancan lokacin jaridar Leadership ta ce El-Mustapha ya ja-kunnen ‘yan jarida su guji yin hira da Abdul Saheer a kan duk wani abin da ya shafi harkar fim a jihar.

Daga karshe dai Jarumi malam Ali ya wallafa bidiyo Yana Bankwana da sana ar dama masanaantar. Tare da fadin dalilan dayasa baibi umarnin hukumar tace Fina finan da censor board saboda Shi ya fita a masanaantar.

Sai dai duk kokarin mu don Jin tabakin hukumar tace Fina finan wato Abba Almustapha Bai dauki wayar mu ba.

 

 

Hafsat Ibrahim