Senegal Ta Doke Masar A Wasan AFCON Ta Karshe Na 2021 

0
168

Senegal ce  kasar da ta ci gasar cin kofin nahiyar Afirka bayan ta doke Masar da bugun fanariti.  Wannan dai shi ne karon farko da Senegal ke lashe gasar kwallon kafa ta nahiyar Afirka mai daraja.  Sadio Mane ya samu galaba a kan abokin wasansa na Liverpool, Mohamed Salah, a wasan karshe, yayin da Senegal ta doke Masar da ci 4-2 a bugun fenareti.

A minti na uku ne aka baiwa Mane bugun daga kai sai mai tsaron gida na Masar.

Ba a zura kwallo a raga a cikin mintuna 90 na yau da kullun ba kuma wasan ya tafi cikin karin lokaci.  Daga nan ne kuma aka tashi wasan karshe na AFCON a bugun fenariti bayan da kungiyoyin biyu suka kasa zura kwallo a raga a cikin mintuna talatin da karin lokacin.

Senegal da Masar za su fafata a gasar cin kofin duniya na Afirka a ranar 23 ga Maris da 29 ga Maris.

 

By: Firdausi Musa Dantsoho