SHUGABA MUHAMMADU BUHARI YA RATTABA HANNU KAN DOKAR GYARAN ZABE NA 2022,WANDA AKA YIWA KWASKWARIMA.

0
130

Shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya rattaba hannu kan kudurin dokar gyaran zabe a zauren majalisar da ke fadar Shugaban kasa a Abuja a yau jumma’a.

Mataimakin Shugaban kasar Ferfesa Yemi Osinbajo, Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan,Shugaban man wakillai Femi Gbajabiamila sun halarci wurin yayin rattaba hannun kan kudurin.

A nasa jawabin, Shugaba Buhari, ya ce a bisa al’ada da aka kafa,ya samu bayanai daga ma’aikatu,hukumomin Gwamnati, da suka dace bayan nazari sosai kan kudirin da kuma tasirin sa ga tsarin dimokradiya a Nijeriya.

Shugaban ya kara da cewa,abin farin ciki ne a lura da cewa,kudirin na yanzu ya zo da gagarumin ci gaba daga kudurin dokar zabe na shekarar 2021 da ya gabata.

Akwai wasu tsare-tsare masu inganci da yabo da za su iya kawo sauyi ga zabuka a Nijeriya, ta hanyar bullo da sabbin fasahohi na zamani.

Wadannan sabbin abubuwa za su tabbatar da ‘yancin tsarin mulki,ya kuma ba ‘yan kasa damar kada kuri’a yadda ya kamata.

Shugaba Buhari ya ci gaba da cewa,kudurin zai inganta tare da samar da haske,inganci da kuma bayyana tsarin gudanar da zaben,tare da rage mafi karancin matsalolin da ke tasowa daga ‘yan takara da Jamm’iyun siyasa da ba su gamsu ba.

Wadannan korafe-korafe abin yabawa ne,dai dai da manufofin na ingantaccen tsarin doka wanda zai share fage na ingataccen tsarin zabe wanda za mu yi alfahari da shi.

A cewar sa,ya ku ‘yan majalisar dattawa da masu girma ‘yan majalisar tarayya, daga nazari na a ra’ayi na,abin da ke cikin kudirin na kawo gyrara ne da kuma ci gaba.ina yin wannan kwakkwaran furucin ne saboda na hango manyan abubuwa da ke cikin kudirin.

Abun lura ya hada da ingancin dimokradiya na kudirin tare da yin la’akari da sashe na 3,9 (2)34,41,47,84,(9)(10)(11)da sauran su.

Fatima Abubakar.