SHUGABAN ƘUNGIYAR GWAMNONIN AREWA INUWA YAHAYA ZAI JAGORANCI LAKCAR TUNAWA DA AHMADU BELLO TARE DA BADA LAMBOBIN YABO

0
9

SHUGABAN ƘUNGIYAR GWAMNONIN AREWA INUWA YAHAYA ZAI JAGORANCI LAKCAR TUNAWA DA AHMADU BELLO TARE DA BADA LAMBOBIN YABO

Shugaban Ƙungiyar Gwamnonin Jihohin Arewa kuma Gwamnan Jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, zai jagoranci taron tunawa da Sir Ahmadu Bello, tare da gabatar da lambobin yabo karo na 10 gobe Asabar a Maiduguri, babban birnin Jihar Borno.

Taron wanda Gidauniyar Sir Ahmadu Bello Memorial Foundation tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Jihar Borno suka shirya, an masa taken “Samar Da Hanyoyin Zaman Lafiya: Yaƙi da Ta’addanci da ‘Yan Bindiga Ta Hanyar Shugabanci na Gari don Ci Gaba Mai Ɗorewa.

Mataimakin Shugaban Ƙasa Sanata Kashim Shettima GCON, da Wakilin Najeriya na din-din-din a Majalisar Ɗinkin Duniya Farfesa Tijjani Muhammad Bande, da ‘yan majalisar ƙasa, da sarakuna da sauran fitattun ‘yan Najeriya ne ake sa ran za su gabatar da jawabai a taron, wanda Gwamna Babagana Umara Zulum zai karɓi baƙuncin.

 

 

 

Hafsat Ibrahim