Gwamna Inuwa Yahaya Ya Lashe Gwarzon Gwamna Na Jarida Telegraph Na 2023

0
14

 

Gwamna Inuwa Yahaya Ya Lashe Gwarzon Gwamna Na Jarida Telegraph Na 202

…’Gwamnan Ya Samu Jinjina Bisa Ƙoƙarinsa A Fannonin Ilimi, Riƙon Amana, Gaskiya Da Nagarta’

Jaridar New Telegraph ta zaɓi Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya CON, don karrama shi da lambar yabo Gwarzon Gwamna na Shekarar 2023 a fannin Ilimi.

A wata wasiƙa mai ɗauke da sanya hannun Manajan Darakta kuma Babban Editan Jaridar, Ayodele Aminu, wacce ta aikewa Gwamnan, jaridar ta New Telegraph ta bayyana cewa Gwamna Inuwa Yahaya ya inganta fannin Ilimi bisa jajircewansa na tsara sabuwar makoma ga jihar, da inganta aikin gwamnati wanda aka gina bisa gaskiya da adalci, da kuma jajircewansa na inganta rayuwar jama’a yasa aka zaɓe shi don bashi lambar yabon mai daraja.

Wasiƙar ta ce “A matsayinka na Gwamnan Jihar Gombe, ka in ganta harkokin Jihar ta kusan dukkan fannonin ci gaban bil’adama da yanayin rayuwa, a rubuce yake cewa a ƙarƙashin kulawarka Jihar Gombe ta samu gagarumin ci gaba a fannin Ilimi, tun daga lokacin da ka shiga harkar siyasa, baka bar kowa cikin shakku ba game da kudurinka na tsara wani sabon tsari a aikin gwamnati, wanda aka gina bisa gaskiya, adalci da kuma kwarin gwiwar inganta rayuwar jama’a.”

Wasiƙar tace irin nasarorin da Gwamnan ya samu a fannin ilimi musamman ginawa da gyaran ajujuwa fiye da 1440 a faɗin jihar; da kwashe yara fiye da 350,000 da ba sa zuwa makaranta zuwa azuzuwa; da inganta makarantun sakandire guda 5 ya zuwa manyan makarantu na musamman, da gina makarantun nakasassu 4 (don kula da masu buƙata ta musamman); da ɗaukar malamai 1,000 da kuma ƙarfafa ilimin sana’a dana fasaha ta hanyar haɗin gwiwa da shirye-shirye daban-daban kamar shirin bunƙasa sana’o’i da Ƙirƙire-ƙirƙire da ake kira IDEAS a taƙaice wanda Bankin Duniya ke tallafawa.

A cewar jaridar ta New Telegraph, waɗannan ayyuka dama ƙarin wassu, sun haifar da ɗa mai ido a fannin ilimi, wanda ya haɗa da ƙaruwar yawan ɗaliban makarantun gwamnati da suke yin nasara a jarabawar kammala sakandare (WASSCE) inda suka ci darusa 5 zuwa sama ciki har da darusan lissafi da Ingilishi daga kaso 28 cikin ɗari a 2019 zuwa kaso 73 cikin ɗari a 2021 da kuma kaso 78 cikin ɗari a 2022, tana mai cewa ayyukan Gwamnan sun zama abin koyi ga takwarorinsa na yankin Arewa Maso Gabas dama Najeriya baki ɗaya.

Da yake karɓar zaɓin, Gwamna Inuwa Yahaya yace wannan karramawar za ta ƙara zaburar da shi da tawagarsa wajen ci gaba da gudanar da ayyukan ci gaba na samar da kyakkyawar makoma ga al’ummar Jihar Gombe ta hanyar samar da ingantaccen ilimi mai rahusa ga al’ummar Gombe.

“Ina matuƙar farin ciki da karɓar wannan zaɓi da naɗin da jaridar New Telegraph ta yi mini a matsayin gwarzon gwamna kan harkokin ilimi na shekarar 2023.

Wannar karramawar ta ƙara jaddada ƙudurinmu na bunƙasa ilimi a jiharmu, ina tabbatarwa Gombawa cewa gwamnatina za ta ci gaba da bunƙasa tsarin iliminmu, wannan karramawar za ta ƙara zaburar da mu wajen samar da ci gaba don samar da kyakkyawar makoma ga ƴan baya masu zuwa ta hanyar samar da tsarin ilimi mai inganci da rahusa.” Inji Gwamna Inuwa.

“Wannar karramawa tana da muhimmaci ga ni kaina da kuma gwamnatina, hakan ya tabbatar mana cewa ana sane da irin ƙoƙarin da muke yi na samar da ci gaba a Jihar Gombe, wannan karramawa daga fitacciyar jaridar New Telegraph, data tantance nasarorin da muka samu a fannin ilimi, zai ƙara zaburar da mu wajen ƙara ƙoƙari kan hidimar da muke yiwa al’ummar mu na inganta ilimi”.

Gwamnan ya ƙara da cewa, wannan karramawa ta sa mu ci gaba da gudanar da ayyukanmu na samar da ci gaba mai girma wa al’ummarmu.

Idan ba a manta ba dai a kwanakin baya ne jaridar The Sun ta zaɓi Gwamna Inuwa a matsayin gwarzon gwamnanta na 2023. Haka kuma, a baya jaridun Vanguard da Leadership ma sun baiwa Gwamna Inuwa Yahayan lambobin yabo na ‘Gwarzon Gwamnan Shekara, don karrama shi bisa ingantacciyar gudumawar da yake bayarwa ga ci gaban tattalin arzikin Jihar Gombe da walwalar al’ummar jihar.

Za a baiwa Gwamnan lambar yabo na jaridar ta New Telegraph ne a wani bikin da aka shirya yi ranar Juma’a 02/02/2024 a ɗakin taro na Balmoral Hall, dake Federal Palace Hotels a Victoria Island, Legas.

Ismaila Uba Misilli
Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe

 

 

 

 

Hafsat Ibrahim