Rundunar sojan Nijar ta ce za ta gurfanar da hambararren shugaban kasar Mohamed Bazoum bisa laifin cin amanar kasa, sa’o’i bayan da kungiyar manyan malaman addinin Islama ta ce masu juyin mulkin kasar a shirye suke su bi hanyar diflomasiyya don warware takaddamar da ke tsakaninsu da kungiyar kasashen yammacin Afirka.
A cikin wata sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na kasar da yammacin jiya Lahadi, kakakin rundunar sojin Nijar ya bayyana tuhumar da ake yi wa Bazoum a matsayin “babban cin amanar kasa da kuma zagon kasa ga tsaron cikin gida da na waje” na kasar.
Bazoum mai shekaru 63 da iyalansa na tsare a fadar shugaban kasar da ke birnin Yamai tun bayan juyin mulkin da aka yi a ranar 26 ga watan Yuli, tare da nuna damuwar kasashen duniya kan yanayin da ake tsare da su.
Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS) ta yi kira da a mayar da Bazoum bakin aiki, tare da kakabawa Nijar takunkumi mai tsauri kan tattalin arziki tare da yin barazanar tsoma bakin soja idan ba a maido da mulkin farar hula ba.
Haka zalika, kungiyar kasashen yammacin Afirka, wadda ta amince da tura wata rundunar ‘yan sanda don maido da tsarin mulki a Nijar, ta ce ta ci gaba da neman hanyar diflomasiyya don warware rikicin.
Kakakin na rundunar sojin Nijar, Kanar Amadou Abdramane, a wata sanarwa da ya fitar ranar Lahadi, ya yi watsi da damuwar da ake da shi kan lafiyar Bazoum, yana mai cewa hambararren shugaban ya ga likitansa a ranar da ta gabata.
“Bayan wannan ziyarar, likitan ya bayyana cewa ba wata matsala game da yanayin lafiyar hambararren shugaban da kuma danginsa,” in ji shi.
Abdramane ya ci gaba da yin kakkausar suka kan takunkumin da kungiyar ECOWAS ta kakabawa Nijar, yana mai cewa matakan “ba bisa ka’ida ba, rashin bin doka da wulakanci” na sanya mutane cikin wahala wajen samun magunguna, abinci da wutar lantarki.
Sanarwar ta zo ne sa’o’i kadan bayan da kungiyar malaman addinin Musulunci ta Najeriya ta sanar da ganawa da jagoran juyin mulkin Jamhuriyar Nijar Abdourahamane Tchiani a Yamai tare da bayyana cewa Janar din ya amince da “tattaunawa kai tsaye” da kungiyar ECOWAS.
Firdausi Musa Dantsoho