Sultan Ya Ayyana Ranar Alhamis 1 Ga Watan Zul Hijjah, Asabar Sallah

0
45
Sarkin Musulmi kuma Shugaban Majalisar Koli ta Harkokin Addinin Musulunci ta Najeriya (NSCIA), Alhaji Muhammadu Sa’ad Abubakar III, ya ayyana ranar Alhamis 30 ga watan Yuni a matsayin 1 ga Dhul Hijjah, 1443AH.
Wannan yana nufin ranar Asabar 9 ga watan Yuli ita ce ranar Eidul Adha ko kuma ranar Sallah, tana zuwa bayan Juma’a 8 ga Yuli, wato ranar Arafat.
A wata sanarwa da kwamitin ganin wata na kasa (NMSC) ya fitar, ya ce Sultan Abubakar ya ayyana ranar Alhamis 30 ga watan Yuni a matsayin ranar daya ga watan Dhul Hijjah.
“Eidul Adha zai kasance ranar Asabar 10th ga Dhul Hijjah 1443H (9 ga Yuli 2022) In Sha Allah.
Mai Martaba Sarkin Musulmi yana kira ga al’ummar Musulmi da su kara himma wajen gudanar da ibada a cikin kwanaki 10 na farkon watan Dhul Hijjah mai albarka. Sannan kuma a yi addu’ar samun zaman lafiya, kwanciyar hankali, da ci gaban kasa, in ji sanarwar.
Daga: Firdausi Musa Dantsoho