TA WANE HANYOYI NE KUKE TUNANIN GWAMNATI ZATA BI WAJEN DAKILE MATSALOLIN TSARO A NIGERIA?

0
172

Jama’an kasar Najeriya sun kasance suna matukar damuwa da yadda gwamnatin kasa da ma na kananan hukumomi zasuyi aiki tare wajen ganin an magance matsalar tsaro dake addabar kasar. A wannan yanayi da kasar Najeriya take ciki matafiyi yana fargaban tafiya domin zai iya dawowa ba rai ko kuma a daurawa yan uwansan nauyin samo kudin karbanshi,Dubbanin mutane da basu jiba basu gani ba sun mutu, anyi asarar kayayyakin kasa da suka shafi miliyoyin kudi, duk sabida gwamnati ta kasa maida mutanen da basuda tausayi da Imani tarihi a kasar. Mutane da dama sun rasa gidajensu sabida waennan azzaluman mutane da suke aikin ta’addanci, babu satin da zai wuce bakaji ance wasu waenda ba’asan ko su wayeba sun shiga kauyuka sun kashe rayuka marasa laifi,waennan yan ta’addan ba aljanu bane toh meyasa baza’a iya kawo karshen suba? Wannan yanayi da ake ciki ya sa kasar Najeriya ta shiga sahun kasa mafi yawan yan ta’adda a duniya, wadda yake nuna cewa ya kamata gwamnati ta kara tashi tsaye duk da cewa a yanxu matsalar tsaro yana kara raguwa wadda a da kasar Maiduguri bata shiguwa amma yanxu an samu sauyin yanayi na matsalar tsaro ta wajen. Amma babban abun dubawa shine matsalar rashin aikin yi ga matasa domin shi ne abu mafi muhimmanci da zai rage ta’addanci a kasar.

Bari muje ga jin ra’ayoyin mutane domin jin hanyoyin da gwamnati zatabi wajen dakile wannan matsala ta tsaro a kasar.

Sadik: sadik yace hukumomin tsaro suna bukatar a wadata su da kayan aiki domin yaki da ta’ddanci a kasar, abunda nake nufi da a wadatasu da kayan aiki shi ne in har an wadata hukumomin tsaro da kayan aiki na zamani matsalar tsaro zai zama tarihi a Najeriya. Wani kalubalen kuma shi ne matsalar cin hanci da rashawa, gwamanati ya kamata ta sake daukan mataki kan matsalar cin hanci da rashawa, kuma a kara kirkiro da hukumomi domin daukan ma’aikata.

              AMINU MISILLI: Aminu yace daukar jami’an tsaro akai akai tare da hadinguiwar al’ummah domin jin baya nai,inganta harkar ilimi,yaki da cin hanci da rashawa, inganta ilimi duk da cewa haqiin duka ba gwamnati kadai ya rataya ba kusan yana kan kowa kama daga iyaye, malamai, da duk wani mai iya fada a ji. sai kuma a kara hukumomin tsaro a kasar. 

 

MUHAMMAD BELLO UMAR: Mhammad umar yace a cire hukumomin tsaro da suke jagorantar garuruwa saboda garuruwan zasu samu Daman rike matsalar tsaron garinsu wadda police zasu samu Daman aiki da kyau kuma kowane gwamna zai samu daman aiki sosai don dakile matsalar tsaron garinsa. 

MUHAMMAD IBRAHIM: Ibrahim yace maganar gaskiya shine a nawa bayanin akwai hanyoyi da dama wanda gwamnati ya kamata ta dauka wajen dakile matsalar tsaro, abu na farko shi ne gwamnatin kasa tare da hukumomin tsaro su hada kai da guiwa don kara tantance border na kasar. Domin saboda yawancin makamai da ake shigowa da su ba bisa ka’ida ba ana kawo su ne ta border.kuma su kansu yan ta’addan suna aika aika ne su gudu wani kasar. Haka zalika gwamnati tayi kokari wajen kawo ayyukanyi ga matasa saboda yawancinsu rashin sana’a ne ya sa suke fadawa ta’addanci domin samun kudin shiga.kuma duk wanda aka kama da hannunsa cikin wani abu da akayi a hukuntashi domin ya zama darasi ga sauran.

 

BY: UMMU KHULTHUM ABDULKADIR