Tarihi Da Kuma Yadda Akeyin Penti A Yadin Shadda.

0
11

Mutane sun kasance suna penti na kayansu shekaru da dama, musamman lokacin da mutane suka fara hada yadi da dinkawa domin hada atampa , masu amfani da penti domin adon jikinsu su ka fara gwadawa a kayayyakinsu,a lokacin aka samu hanyoyi biyu wato saka hoto da kuma zuba kala wato akan kayan, sai kuma fidda kala tare da hoto. A lokacin kasar asia tana dogon tarihi na pentin kaya, amma an fara zanen kaya da painti a lokacin shekara ta alib 3000 a kasar india a ka fara samun penti na zane. Baya an fara samun harkan shige da fice na sai de sai den kaya masu zanen penti suka fara shiga kasashen asia, Egypt da kuma Greece, bayan wasu shekaru kuma aka samu hanyan shigo dasu afirka. Da haka kuma kasar china ta fara fidda itama nata zanen pentin cikin kaya. Haka zalika aka fara samun basira wajen zanen penti a kaya a duniya gaba daya wanda a ynxu ya koma kayan da muka fi so da kuma sha’awa kamansu batik,shadda da kuma rini a wannan zamin kuma har aka koma yin penti a jikin shadda na adon mata.Wadda a ynxu zamuyi Magana ne akan penti na shadda da kuma rini

In zakayi penti ana bukatan ka zabi yadi mai kyau ta yadda kyau da kwalliyan pentin zai fito sosai a jikin yadi. Don haka zabi na yadi mai kyau yanada amfani sosai Kaman yadi me laushi, shadda na getzner da sauransu.

Haka zalika akwai abubuwa masu muhimmanci wanda mutum ya kamata ya rike wajen yin penti na shadda ko kampala, samun yadi mai kyau shi ne zai fitar maka da yanayin penti yadda ya kamata, kamar ynxu irin getzener da ake yayi wanda ruwa baya jikashi, wannan yadi na getzner bazai dau penti ba sabila da ruwa baya zama a kanshi kuma kun san penti dole sai an kwabashi da ruwa. Haka zalika abun dubawa na biyu shine  yanayin yadi shi ne zai nuna maka wane irin penti zakayi dashi domin kuwa akwai shadda da bazaa iya rina ta gaba daya ba sai dai a yi penti a kowane sassa nata da ado mai kyau.

Kafun yin penti a jikin shadda ana bukatar a fara wanketa saboda ya zama duk wani starch ya fita a jikinta. Kuma ana bukatan yadin ya zama ya bushe kuma an goge shi.idan har akayi waennan abubuwa toh shine ya nuna cewa yadinka ya zama ready a mishi penti

Kayan yin penti sune kamar haka:

Brush

Soso

Soson wanke baki

rubber na sa  ruwa

bokiti mai mufi

rigan girki domin killace kayan jikinka

na takarda tsumma

ana iya saka penti a shadda ta hanyoyi daban daban Kaman:

Amfani da abun zane:  Ana daukan takarda mai kauri  sai kayi zanen da ranka yakeso wanda kakeso kaga ya fito kan shadda naka in ka zana sai ka yankashi ta inda in ka manna kan shadda naka zaka iya bi ba tare da ka bat aba. Zaka iya amfani da brush wajen shafa fentin zakuma ka iya amfani da soso.

Saka kaloli: Wannan shine akebi wato ta hanyan rini kenan, zaka iya nade yadi naka ta inda kakeso adon ya fito, ana iya amfani da igiya ko kuma robali wajen daure duk inda baa so ya fito, haka zalika ana iya amfani da abu a zana shi in an gama sai a rufe zanin da zaa rina dashi sai a saka in an fito sai a cire zai firo irin kalan zanen da aka masa sai a shanya shi ya bushe.

Paintin rana: Ana yin penti akan rana penti wajen rana abune mai sauki yana amfani ne da karfinn hasken rana wanda zai kayata zanenka.zaka dau yadinka da kakeson yin penti a kai Ka dauko ganye ko gashin tsuntsu , fulawa da sauransu, zaka daura ganyenka akan yadin sai kabi da penti ta yadda shape din ganyen yake sai ka ajiye a setin rana har ya bushe in har aka cire ganyen zanen zai fito ne irin launin ganye. Hakan zai iya nuna cewa Kaman inji ne ya zana ba mutum ba.

Penti na gishiri :Ana amfani da gishiri wajen yin penti, bayan an gama zuba penti a jikin yadi sai a dauko gishiri a lokacin da yadin bai busheba sai a barbada shi ta waje daban daban sai a shanya in komi ya bushe sai a dauko yadin a karkade gishirin shima yana fidda ado na kampala mai kyau da kuma burgewa, zaka iya amfani da kaloli daban daban wajen yin pentin saboda kampalan ta fito da kyau./

AMFANI DA TAMBARI WAJEN PENTI: Ana iya amfani da tambari wajen penti kala kala wato yanayin yadda ka zana tambari naka iya yanayin yadda penti naka zai fito kenan, zaa baza yadi a kasa sai a ajiye penti a gefe sai ana daukan tambarin ana donawa cikin pentin sai a manna a kaya har ya bushe,Wannan shine  mafi sauki a wajenyin penti.

UMMU KHULTHUM ABDULKADIR.