Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar, Ya sai fom na tsayawa takaran shugabancin Kasa

0
184

Jamm’iyar PDP a taron ta na majalisar zartarwa ta kasa da ta gudanar a Abuja da yammacin larabar da ta gabata, ta bayyana cewa zata gudanar da taronta na kasa domin tantance Dan takarar ta na shugaban kasa a zabukan 2023.An tsayar da ranar 28 zuwa 29 ga watan mayun 2022.

Kungiyar ta kuma sanya 21 ga watan mayun 2022 domin kaddamar da zaben fidda gwani na gwamnoni da za su yi.

Jamm’iyar ta kuma amince da ka’idojin gudanar da zabukan fitar da gwani na dukkan mukamai, inda ta kayyade fom din takarar shugaban kasa a kan Naira miliyan 5,sannan ta mika Fom miliyan 35.

Amma kungiyar har yanzu bata tsaida wurin da za su gudanar da zaben fidda gwani na shugaban kasa ba.

Kungiyar ‘yan kasuwan Arewa maso Gabas karkashin jagorancin shugaban ta Alhaji Abubakar Dalhatu,ta sai wa Atiku Abubakar fom din tsayawa takara.

Kungiyar ta ce,ta sayi fom din domin cika alkawarin da ta yi wa Atiku a watan Nuwamban 2021.

A jiya ne,aka samu labarin cewa,Atiku zai yi shelar tsayawa takara a zaben 2023 a ranar laraba mai zuwa a Abuja.

By Fatima Abubakar