Hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta kame tsohon Gwamnar Anambra Willie Obiano.

0
59

Gwamnan Obiano wanda ya shafe watanni yana cikin jerin sunayen da  hukumar ta EFCC ta ke fako.

By Fatima Abubakar

An kama tsohon Gwamnar da misalin karfe takwas da rabi na daren Alhamis a filin jirgin saman Legas akan hanyar sa ta zu Houston ta jahar Texas ta kasar Amurka bayan mika kujerar sa ga magajin sa Mr Charles Soludo.

Mr willie dai tun Nuwamban 2021 ne hukumar ta Cin hanci da rashawa ta mika sunan Obiano ga hukumar shige da fice ta Najeriya domin ta sanar da ita duk lokacin da Gwamnar zai fita daga kasar ta kowace filin jirgin sama na kasa da kuma sauran wuraren shige da fice.

Sai dai har yanzu ba a san dalilin da ya sa aka cafke shi ba.

Hakan yayi dai-dai da lokacin Ya mika karagar mulkin Anambra ga magajin sa Gwamna Charles Soludo,inda rikici ya barke tsakanin matar Obiano Ebelechukwu da matan marigyayi Odumegwu Ojukwu wato Bianca,inda Bianca ta shara mata mari a bainar jama’a,inda ita kuma Ebelechukwu ta ke zagin Bianca da munanan kalamai,wanda  anan take jami’an tsaro suka shiga tsakani.Har ikawo yanzu ba.mu san mafari ba.