
Kowani tafin kafa yana da magudanar zufa 250,000 kuma a kowacce rana yana fitar da zufa kofi mil dari biyar [500ml]. yawan zufa hade da bacteriya kan iya jawo warin kafa.
Warin tafin kafa watto smelly feet a turance matsalan kiwon lafiya ne wadda taruwan yawan zufa dake gina bacteriya a tafin kafa ke haifarwa. Wannan bacteriyan na haifar da tsanannin wari. Haka zalika ko masu tsafta ma, na iya fama da wannan matsalan warin kafan.

Domin hana yaduwan bacteriya da kuma magance matsalan warin kafa, dole a magance matsalan yawan zufa a tafin kafa, saboda haka muka kawo maku hanyoyi mafi sauki wajan kawar da matsalan warin kafa.
1. Yin amfani da sabulu marasa karfi wajan wanke kafan.
2. Shafa spirit a tsakanin yatsun kafa sau biyu zuwa uku a rana yana taimakawa wajan busar da fatan kafan ta yanda bazaiyyi zufa sosai ba.

4. A yawaita chanja safan kafa ga masu zuwa makaranta ko yawan son sa safan kafa.

5. A dinga shafawa ko shan antibiotics domin kashe kwayoyin bacteriya da ke taruwa a tafin kafan.
6. Idan har duk abubuwan da muka lissafo basu kawar maku da warin kafa bat oh a tuntubi likita.
Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho