Wa Ya Kamata Yayi Kayan Daki Miji Ko Amarya?

0
393

 

Kamar yadda muka samu Daga shafin  Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa inda ya fayyace mana dalla dalla wa ya kamata ya yi kayan daki tsakanin miji da mata. Haka zalika mu ma muka kawo wa masu karatu wannan bayanin domin karuwan mu gabaki daya.

WA YA KAMATA YA YI KAYAN ƊAKI?

 An daɗe ana ana kai ruwa rana tsakanin ma’aurata akan waye yake da alhakkin yiwa mace kayan ɗaki? Mijin ta ko ita amaryar daga cikin sadaƙin ta? ko kuma iyayanta? Ko kuwa dukkan su kowa yana iya yi? Sannan kayan ɗaki al’ada ne, ko addini? Kyautatawa ne ko dole ne? Bisa haka muka duba maganganun malamai magabata gamai da wannan batu wanda yaƙi ci yaƙi cinyewa, kuma a wasu yankuna ya zama kamar wajibi wanda wasu har bashi suke ɗauka domin su fita kunyar ƴaƴansu, domin kada ya zama abin gori da magana tsakanin dangi. A wasu al’adu da garuruwa da ƙabilu yin kayan ɗaki haƙƙin miji ne, wajibi ya tanadi dukkan abinda ake buƙata a gida, kamar shinfiɗa, da kujeru, da kayan kicin, da dukkan abinda ake buƙata a cikin gida, domin shari’a cewa tayi miji ya bawa mace wajan zama, ba a ɗora mata yin wani abu ba daga cikin sadaƙinta, ko iyayanta.

Wasu al’adu kuma sun ɗorawa amarya da iyayanta yin dukkan kayan gida, abinda miji zai yi kawai ya tanadi gida amma duk abinda za a saka a gidan ɓangaran mace ne zasu kawo, shi yasa idan aka sami matsala aure ya mutu, suke zuwa su kwashe kayansu gaba ɗaya, ko shara ba sa bari. Wasu kuma al’adun suna raba kayan gida kashi biyu, wani miji ya kawo wani kuma amarya ta kawo, akan haka ne idan an sami matsalar aure, ake zuwa a tantance kayan miji da na matar, har shari’a take shigowa kamar yadda mai littafin Tuhfatul Hukkam ya kawo.

FATAWOWIN MALAMAI AKAN KAYAN ƊAKI AKAN WA YAKE?

Gamai da maganganun malamai kuwa akan wannan lamari shine mafi yawan malamai kamar Hanafiyya da Shafiiyyah, da Zahiriyya (Ibn Hazmin), sun tafi akan kayan amfanin gida akan miji yake. Shi zai tanadi dukkan kayan buƙatu da amfani na gida ba amarya ba ko iyayan ta, domin tsoran kada a taɓa mata Sadaƙi wajan siyan kayan (kamar yadda yake faruwa da yawa a cikin hausawa, suna yiwa amarya kayan ɗaki da sadaƙin ta). Wasu kuma cikin Malaman suna ganin idan iyayan amarya suka yi kayan ɗakin saboda kyautatawa babu laifi, saboda Hadisin Sayyadina Aliyyu RA lokacin da ya auri Nana Fatimah RA, Manzon Allah saw ya yi musu kayan ɗaki (katifah da filo da tukunya) Ibn Majah ya ruwaito. Don haka yin kayan ɗaki kyautatawa ne ba wajibi bane akan iyaye idan suna da hali su yi daidai gwargwado, kada a dinga cin bashi ana shiga rigima don yin kayan ɗaki.  Mun samu bayyanan nan Daga Shafin Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa Kano na facebook.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho