Wani bala’i ya afku a ranar Talata a bakin tekun Elegushi da ke unguwar Lekki a jihar Legas, bayan da wasu matasa hudu suka nutse a ruwa a lokacin da suke lyo a cikin ruwa.
An tattaro cewa dalibal 10 da suka kammala karatun sakandare, masu shekaru tsakanin 14 zuwa 15, sun je yin iyo a bakin ruwa domin murnar kammala jarrabawarsu ta manyan makarantura: yammacin Afirka.
An ce su daliban babbar kwalejin Kuramo ne da keĀ Lekki.
Mai magana da yawun hukumar kula da bakin tekun Elegushi, Cif Ayuba Elegushi, a wata sanarwa da ya fitar ranar Talata, ya ce daliban ba su yi rijistan shiga wurin ba.
Ya lura da cewa lamarin ya faru ne a wani sashe na bakin teku da ba a bude kofa ga jama’a.
Ya ce, “Da farko mun sallame su daga yankin gabar tekun da suke son yin iyo, daga nan suka tafi wani wurin da ba na jama’a ba,anan ne lamarin ya auku,inda mata biyu da maza biyu suka nutse cikin ruwan wanda kawo yanzu ba a samo gawawwakin su ba.
Har ila yau a jahar Sakkwato wata dalibar Khalifa International school sokoto, ta rasa kafar ta yayin da wasu dalibai ke wasan gudu da mota inda suka ka hau kan kafafun ta.Wanda a sanadiyar hakan aka yanke mata kafa daya a asibiti.
Wani iyaye mai suna malam Ahmad ya dora alhakin irin faruwar hakan akan iyaye ma su bawa yayan su motoci suna hawa ba bisa ka’ida ba.ya yi kira ga iyaye ,malamai,hukuma da har ma Gwamnati da ta dauki tsatsauran matakai domin hana irin wayannan shagulgula yayin kare makarantu domin ya zama ruwan dare.
Daga Fatima Abubakar