Wasu yan bindiga sun kai hari cibiyar horaswa na INEC a Anambra

0
25

 

Wasu ‘yan bindiga da ba a san ko su waye ba sun kai hari  makarantar sakandare ta Ukpor  wurin da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ke horaswa a karamar Hukumar Nnewi ta Kudu, Jihar Anambra, da yammacin ranar Alhamis.

Maharan sun kawo cikas wajen gudanar da ayyukan horaswan gabanin babban zaben shekarar 2023.

Wata majiya a unguwar ta ce lamarin da ya faru da misalin karfe 5:35 na yamma, ya sanya daliban da jami’an hukumar NYSC da sauran wadanda ke halartar horon cikin rudani.

“Ina shakkun ko mutanen za su amince su yi wa INEC aiki a yankin. Amma mun gode wa Allah da ba a kashe kowa a cikin lamarin ba. Lamarin ya sa ni cikin rudani. Ba mu da tabbacin wadannan mutanen za su ba mu damar yin aiki mako mai zuwa,” inji majiyar.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Anambra, DSP Tochukwu Ikenga, wanda ya tabbatar da rahoton, ya bayyana cewa jami’an sun hana maharan yin garkuwa da su ko kuma cutar da wadanda ake horas da su.

Ya ce, “Bisa dabarun aikin ‘yan sanda da Kwamishinan ‘yan sanda, CP Echeng Echeng ya gindaya, wanda ke da karfi da kuzari wajen mayar da martani ga duk wata matsala ta gaggawa da tsaro musamman tabbatar da zaben 2023 wanda ba shi da cikas a jihar, kungiyar tsaro ta hadin gwiwa. yau 16/2/2023 da karfe 5:35 na yamma sun yi nasarar ceto tare da hana wasu ‘yan bindiga cutar da jami’an zabe a wani aiki a makarantar sakandare ta Ukpor, karamar hukumar Nnewi ta Kudu.

“Ma’aikatan INEC tare da wasu ‘yan kungiyar corps, daliban jami’a da kuma wasu jami’an MDA kan shirin horas da ma’aikatan Adhoc domin gudanar da zabukan 2023 da ke tafe, ‘yan bindiga sun hargitsa su. Ba a rasa rai ba.

“An karfafa jami’an tsaro na hadin gwiwa a yankin kuma ana ci gaba da kokarin zakulo masu aikata laifuka. Za a sanar da ƙarin ci gaba, don Allah.”

 

Daga:Firdausi Musa Dantsoho