Mu Ba Masau kudi bane, Na Nemi Naira Miliyan Biyu A Wajan Matar Shettima  A Jiya – Remi Tinubu

0
91

SANATA Oluremi Tinubu, uwargidan dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar All Progressives Congress, Bola Tinubu, ta bayyana cewa ta roki matar abokin takarar mijinta, Hajiya Nana Shettima naira miliyan biyu a ranar Laraba.

Jaridar News Point Nigeria ta ruwaito cewa, Oluremi ta fadi hakan ne domin nunawa wasu da dama da suke ganin cewa iyalanta suna da arziki kuma mijin nata ya shahara ne saboda arzikinsa.

Oluremi, tsohon Sanatan jihar Legas ne ta bayyana hakan a ranar Alhamis, yayin wani taro da aka yi da nakasassu a Abuja.

“Idan suka ce yana da arzikin duniya, sai in yi mamaki. Misis Shettima ta san cewa na roke ta N2m jiya,” inji ta.

Ta danganta karamcin da Tinubu ya ke yi ne a matsayin dalilin farin jininsa ba kudi ba. Oluremi ya ce, “Sirin Asiwaju bai shi da alaka da kudi, sabanin yadda mutane ke tunani, mutum ne mai tausayi da yawan kyauta. Babu abin da ba zai iya bayarwa ba.”

“Na tuna bayan ya gama gwamna, muna da wannan ma’aikaci a gida; idan kana bukatar wani abu, sai ya ce ka je ka samu wannan da wannan haka yake.

“Mutanen da kuke gani a gangamin sa ba wai suna bayan kudi ba ne. Sun yi imanin wani zai iya ba su bege a cikin waɗannan lokutan wahala. ”

Tinubu na daya daga cikin manyan ‘yan takarar da ke neman zama shugaban kasar Najeriya a babban zaben da ke tafe a ranar Asabar mai zuwa.

 

Daga:Firdausi Musa Dantsoho