Mummunan Zanga-zanga Ta Barke A Legas Kan Sabbin Naira

0
79

 

Zanga-zangar ta barke a wasu yankuna a kan babbar hanyar Legas zuwa Ikorodu a jihar Legas saboda karancin sabbin kudin Naira da kuma wahalhalun da manufar ta jefa ‘yan Najeriya.

A safiyar ranar Juma’a ne, News Point Nigeria ta tattaro cewa masu zanga-zangar a Mile 12, Ketu da Ojota a kan titin, sun nufi hanyar suna far wa matafiya tare da haifar da hargitsi.

Wani direban mota da ke da alaka da daya daga cikin kamfanonin mota da ke aiki a jihar wanda baya son a bayyana sunansa saboda fargabar tsangwama, ya ce sai da ya koma daya daga cikin tituna saboda hargitsin.

Wata majiya ta shaida wa News Point Nigeria cewa, wasu da ake zargin yan dabba ne suka fara lalata shaguna da ofisoshi a yankin.

Wasu shaidun gani da ido, wadanda suka ba da cikakken bayani kan fadan da ake ci gaba da yi a yankin, sun yi zargin cewa suna jin karar harbe-harbe.

A halin da ake ciki, jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Legas, Benjamin Hundeyin, ya tabbatar da tashin hankalin da ke faruwa a yankin Mile 12 na jihar Legas.

Ya bayyana hakan ne ta shafin sa na Twitter a safiyar Juma’a.

Da yake mayar da martani ga wani sakon Twitter da ya nemi PPRO ya tabbatar da jita-jita, Hundeyin ya amsa, “Gaskiya ne. Mutanenmu suna can. An tura sassan ƙarfafawa. A zauna lafiya a can yayin da muke sa ido sosai da sarrafa lamarin.

 

Daga:Firdausi Musa Dantsoho