Wasu ‘yan bindiga sun kashe mutum 1,sun jikkata 1,tare da sace mutum 7 a kan titin Arab da ke gundumar Kubwa

0
74

Wasu ‘yan bindiga da ake kyautata zaton masu garkuwa da mutane ne a daren ranar Talata sun kai hari a unguwar Arab Road Extension 2 da ke gundumar Kubwa a cikin babban birnin tarayya Abuja, da yammacin ranar Talata, inda suka yi garkuwa da wani ma’aikacin kungiyar matasa mai suna Adenike da wasu bakwai tare da kashe wani mazaunin garin.

Majiyoyi sun ce an yi garkuwa da Miss Adenike wadda ita ce kadai yar iyayenta a lokacin da ‘yan bindigar suka far wa wasu gine-ginen da ke kan titin Arab inda suka yi ta harbe-harbe tare da lallasa duk wani mazaunin da za su iya kamawa ya bi su.

An ce mutane biyu ne suka samu harbin bindiga wanda ya yi sanadiyar mutuwar daya a nan take yayin da dayan kuma aka garzaya da su asibiti bayan da ‘yan fashin suka yi awon gaba da wadanda aka sace.

Majiyoyi sun ce ‘yan bindigar sun samu shiga titin Arab ne daga wani tudu da ke zama matsuguni ga mazauna yankin.

“Baya ga matashin , muna neman wasu mazauni guda bakwai. Babu wanda ke iya barci kuma. Kamar yankin yaki ne yadda suke harbi. An yi sa’a biyu daga cikin wadanda aka sace sun tsere. A haka muka san an tafi da mutane bakwai,” inji wani mazaunin garin.

“Daga titin Amilomania, sun koma Toyin Street, duk a cikin Extension 2 Relocation, a kan titin Arab, a Kubwa” majiyar ta kara da cewa “daya daga cikin wadanda aka harben har lahira wani shahararren tela ne a yankin.

Majiyar ta ce ta yiwu ‘yan fashin sun koma yin amfani da yankin tuddai ne domin samun damar shiga titin domin kaucewa ‘yan banga da ke jibge a babbar kofar shiga titin, don gujewa kar a gan su.

Kokarin da aka yi na ganin jami’an ‘yan sandan babban birnin tarayya, DSP Josephine Adeh ya yi tsokaci kan lamarin a daren jiya ya ci tura.

 

Daga Fatima Abubakar.