Jaruma rahma sadau tayi murnar cika shekaru 29

0
186

 

Fitacciyar jarumar rahma sadau ta cika shekaru 29 da haihuwa.
Jarumar wanda ta kasance fitacciya kuma ake damawa da ita a kamfanin shirya fina finan hausa ta Kannywood da kuma na turanci nollywood ta cika shekara ne a ayau 7 ga watan December 2022.

Jarumar ta wallafa kayattattun hotunan ta, tare da rubuta kalaman yabawa kai da godiya ga ubangiji Allah.Jarumar tayi rubutu kamar haka da harshen turanci muka fasara;

“Babi na 29
Ina taya kaina murnar cikan shekara.
Rahama Kyakyawa, jajirtacciya, mai karfi dq cike da abun mamaki.
Akwai Abubuwan Da Yawa Don Yin Godiya akai, Amma Ba abun da ya fi kasancewa da rai, Lafiya da Farin Ciki.

Alhamdulillah barkanmu da ganin wani Shekara mai albarka.

Ya Allah, nagode Da ni’iman ka a gareni. “

Jarumar ta zamun duban masoyanta har ma da abokanayan aikinta waenda suka taya ta murnan cika wannan shekaran mai Albarka.

Manajan tozali da ma’aikatan ta na taya rahma sadau cika shekara da kuma yin mata fatan alkhary.

Daga:Firdausi Musa Dantsoho