Wani mamba na rundunar yan banga Isah Hamma Joda, ya auri Diana Maria Lugunborg, ‘yar kasar Norway a jihar Adamawa, a karshen makon nan.
An ce Lugunborg ta miki gari zuwa Adamawa domin aure matashin.
An gudanar da liyafar ne a kusa da kwalejin nazarin shari’a da ke karamar hukumar Yola ta Arewa.
Da farko dai ma’auratan sun daura auren ne a babban ofishin rajistar babbar kotu da ke Yola.
Ba a dai san yadda suka hadu ba amma akwai rahotannin cewa ya kasance a shafukan sada zumunta.
Ga hotuna a kasa:
Firdausi Musa Dantsoho