Gwamnan Kano Ya Nada Jarumi AlMustapha A Matsayin ES Na Hukumar Tace Fina-Finai, Da Sauran Shugabannin Hukumomi 13.

0
44


Gwamnan jihar KANO, Abba Kabir Yusuf wanda aka fi sani da Abba Gida Gida ya nada jarumin Kannywood, Abba AlMustapha a matsayin babban sakataren hukumar tace fina-finai ta jihar Kano tare da wasu shugabannin hukumomin gwamnati 13.

A cewar wata sanarwa da babban sakataren yada labarai na gwamnan jihar Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar a ranar Laraba, nade-naden na nan take.

Sanarwar ta kara da cewa:A ranar Laraba 19 ga Yuli, 2023 Gwamnan Jihar Kano Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf ya amince da nadin shugabannin hukumomin gwamnati. Wadanda aka nada sune kamar haka.

  1. Ado Ibrahim Umar, Manajan Darakta na Kamfanin Raya Wutar Lantarki ta Kano (KHEDCO)
  2. Auwalu Mukhtar Bichi, Manajan Darakta, Kano State Investment and Properties Limited (KSIP).
  3. Farouq Kurawa, Manajan Daraktan Hukumar Noma da Raya Karkara ta Jihar Kano (KNARDA). Har zuwa lokacin da aka nada shi, Dakta Kurawa shi ne Babban Sakataren Gwamnati (PPS) na Gwamna.
  4. Tukur Dayyabu Minjibir, Manajan Daraktan Kamfanin Samar da Aikin Gona na Kano (KASCO).
  5. Hussain Sarki Aliyu Madobi, Manajan Director, Sustainable Kano Project (SKP)
  6. Sadiq Kura Muhammad, Manajan Darakta na lambun dabbobin Kano (ZGK)
  7. Sani Bala, Manajan Daraktan Hukumar Lantarki ta Karkara (REB)
  8. Shamwilu Gezawa, hukumar samar da ruwan sha da tsaftar muhalli ta jihar Kano (RUWASA)
  9. Tukur Bala Sagagi, Manajan Darakta na hukumar yawon bude ido ta jihar Kano 10. Alh. Yahaya Muhammad Idris Manajan Daraktan Kamfanin Buga na Jihar Kano
  10. Adamu Yahaya, Mataimakin Manajin Darakta (DMD), Kamfanin Buga na Kano
  11. Abba El-mustapha, Babban Sakataren Hukumar Tace Fina-Finai ta Jihar Kano
  12. Muhammad S. Khalil, Babban Sakatare na Hukumar Kula da Sauyin Yanayi ta Jihar Kano (KN-WECCMA).
  13. Dahir M. Hashim, Kodineta na Hukumar Kula da Canjin Ruwa ta Jihar Kano (KN-WECCMA).

Ana umurtar duk wadanda aka nada da su fara aiki nan take.

Ina taya ku murna Sanusi Bature Dawakin Tofa Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamnan Jihar Kano Mai Girma Alhaji Abba Kabir Yusuf.

Firdausi Musa Dantsoho