Wata Budurwa Yar Kasar Norway Ta Zo Najeriya, Ta Auri Dan Banga A Jihar Adamawa

0
92

Wani mamba na rundunar yan banga Isah Hamma Joda, ya auri Diana Maria Lugunborg, ‘yar kasar Norway a jihar Adamawa, a karshen makon nan.

An ce Lugunborg ta miki gari zuwa Adamawa domin aure matashin.

An gudanar da liyafar ne a kusa da kwalejin nazarin shari’a da ke karamar hukumar Yola ta Arewa.

Da farko dai ma’auratan sun daura auren ne a babban ofishin rajistar babbar kotu da ke Yola.

Ba a dai san yadda suka hadu ba amma akwai rahotannin cewa ya kasance a shafukan sada zumunta.

Ga hotuna a kasa:

Firdausi Musa Dantsoho