Yadda aka Ƙaddamar da baje Kolin Kasuwancin cikin Gida na Arewa maso Gabas karo na 15

0
12

Daga Yunusa Isah kumo

An Ƙaddamar Da Baje Kolin Kasuwancin Cikin Gida Na Arewa Maso Gabas Karo Na 15 A Bauchi

…Inda Gombe Ta Buɗe Rumfarta, Ta Kuma Yi Gagarumin Baje Koli Gabanin Ranar Gombawa Da Za A Yi Ran Laraba

Gwamnan Jihar Gombe Muhammadu Inuwa Yahaya CON, tare da wasu shugabannin Arewa Maso Gabas, sun bi sahun Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima wajen ƙaddamar da bikin baje kolin hada-hadar kasuwanci na cikin gida karo na 15 na Shiyyar Arewa Maso Gabas a Bauchi.

 

Taron dai na daga cikin dabarun da ƙungiyar gwamnonin shiyyar ta ƙirƙiro don farfaɗo da harkokin kasuwanci da cinikayya a yankin wadda rikicin tada ƙayar baya ya yiwa illa, don nausa jahohin yankin 6 ga ci gaba mai ɗorewa.

 

Jihar Gombe, wacce ta shahara a matsayin cibiyar kasuwancin Arewa Maso Gabas, ita ce kuma jihar da ta fi fice a Najeriya a fagen sauƙaƙa kasuwanci, inda ta kafa wata rumfa mai ban sha’awa a harabar kasuwar baje kolin.

 

Dukkanin ƙananan hukumomi 11 na Jihar Gomben sun baje kolin kayayyakinsu na noma da albarkatun ma’adinai daban-daban musamman waɗanda suka fi ji da su a yankunansu don jawo masu zuba jari ta hanyar nuna ɗimbin damammakin da jihar ke da su.

 

Suma ’yan kasuwan jihar Gomben ba a barsu a baya ba wajen halartar bikin baje kolin kasuwancin, lamarin da ke nuni da yanayin kasuwancin da jihar ke da shi.

Ismaila Uba Misillib

Babban Daraktan Yaɗa Labarun Gwamnan Jihar Gombe.

 

 

 

 

Hafsat Ibrahim