Yanna da gundura ace a ko da yaushe idan mutum zai ci plantain sai dai ya soya ko kuma ya dafa, shiyasa yau zamu kawo maku watta sabuwar hanya da zaku bi domin jin daddin plantain inku a sauwake kuma ba sai kun kasha kudi ba.
Ana kiran wanan hadin battered plantain.
ABUBUWAN BUKATA SUNE:
- Plantain
- flawa
- Kwai
- Baking soda dan kadan
- Sinadarin dandano
- Yaji
- Gishiri
- Man gyada
YADDA AKE HADAWA
- A cikin kwanu mai tsafta mu fasa kwan mu a ciki, sai mu zuba sinadarin dandanon mu, yaji, gishiri, baking soda sai mu juya ya hadu.
- A cikin haddin kwan, mu zuba flawa da dan ruwa sai mu juya har sai komai ya hadu kuma hadin yayyi kauri.
- Sai mu bare plantain, mu yanyanka shi shape in da muke so.
- Sai mu tsoma plantain in mu cikin kwabin flawa, mu tabbatar flawan ya kama plantain in sosai.
- Daga nan sai mu sa plantain in mu da muka rufe kwabin flawan cikin man gyada mai zafi mu soya .
- In plantain in yayyi brown sai mu kwashe.
- Toh battered plantain in mu ya haddu. Aci lafiya.
Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho