YADDA AKE HADDA BATTERED PLANTAIN

0
838

Yanna da gundura ace a ko da yaushe idan mutum zai ci plantain sai dai ya soya ko kuma ya dafa, shiyasa yau zamu kawo maku watta sabuwar hanya da zaku bi domin jin daddin plantain inku a sauwake kuma ba sai kun kasha kudi ba.

Ana kiran wanan hadin battered plantain.

ABUBUWAN BUKATA SUNE:

 • Plantain
 • flawa
 • Kwai
 • Baking soda dan kadan
 • Sinadarin dandano
 • Yaji
 • Gishiri
 • Man gyada

YADDA AKE HADAWA

 1. A cikin kwanu mai tsafta mu fasa kwan mu a ciki, sai mu zuba sinadarin dandanon mu, yaji, gishiri, baking soda sai mu juya ya hadu.
 2. A cikin haddin kwan, mu zuba flawa da dan ruwa sai mu juya har sai komai ya hadu kuma hadin yayyi kauri.                                 
 3. Sai mu bare plantain, mu yanyanka shi shape in da muke so.
 4. Sai mu tsoma plantain in mu cikin kwabin flawa, mu tabbatar flawan ya kama plantain in sosai.                                                   
 5. Daga nan sai mu sa plantain in mu da  muka rufe kwabin flawan cikin man gyada mai zafi mu soya .
 6. In plantain in yayyi brown sai mu kwashe.
 7. Toh battered plantain in mu ya haddu. Aci lafiya.

 

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho