YADDA AKE HADDA CHOCOLATE CUPCAKE

0
1563

Chocolate cupcake, cake ne amma na chocolate kuma cake ne da ake yinsa a kananan kofin hada cake, yana da zaki ga daddi ga kuma saukin hadawa.

ABUBUWAN BUKATA SUNE:

 • Flawa kofi biyu
 • Siga kofi daya da rabi
 • Cocoa powder kwatan kofi
 • Kwai guda biyu
 • Vanilla flavour cokali daya
 • Man gyada rabin kofi
 • Madara kofi daya
 • Nescafe dan kadan
 • Bakar hoda cokali daya
 • Baking soda cokali biyu
 • Ruwa kofi daya

YADDA AKE HADAWA

 1. Da farko zamu samu roban mu mai tsafta sai mu zuba flawan mu kofi biyu, siga kofi daya da rabi, bakar hoda cokali daya, baking soda cokali biyu, sai mu juya su gabaki daya.
 2. Daga nan sai mu zuba cocoa powder kwatan kofi sai a kara juya wa, wannan hadin su ake kira dry ingredients.                                       
 3. A cikin wanni kwanu daban mu zuba madaran mu na ruwa kofi daya, man gyada rabin kofi, kwai guda biyu sai mu juya, wadannan sune wet ingredients.
 4. Sai mu dauko hadin madaran mu watto wet ingredients, mu zuba acikin hadin flawan mu watto dry ingredients sai mu juya domin komai ya hade da kyau. 
 5. Idan komai ya hade zai mu zuba flavour in mu.
 6. A cikin tafashashen ruwan kofi daya mu sa nescafe dan kadan, mu juye a cikin kwabin cake in mu .                       
 7. Mu tabbatar muna juye tafasashen ruwan, mu juya shi agurguje domin kar yayyi gudaji.
 8. Sai mu samu tray in cup cake in mu, mu sa cupcake paper in mu, sai mu zuba rabin kofin kwabin cake in mu a cikin kowanni cupcake paper .           
 9. Sai mu sa, a oven mu gasa na minti ashirin, toh chocolate cupcake in mu ya hadu.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho