YADDA AKE HADDA CORN DOG

0
860

Da farko de shi corn dog ba da naman kare ake yinsa ba domin wasu idan suka ji corn dog sai su zata naman kare ne, corn dog ana yinsa ne da sausauge, wadda shi kuma sausauge in nikakken nama ne na kaza ko rago.

A fayyace, Corn dog de sausage ne da ake sakawa a tsinke a kuma rufe shi da hadin flawa sai a soya shi, ya samo asali ne daga kasar amurka kuma yana daya daga cikin abincinsu.

ABUBUWAN BUKATA WAJAN HADA CORN DOG SUNE:

  • Sausage
  • Flawa
  • Corn flour cokali 2
  • Sigar rabin kofi
  •   kwai 1
  •   Bakar hoda cokali 1
  •  Milk kofi 1
  •  Gishiri kadan
  •  Tsinken tsire skewer

YADDA AKE HADA CORN DOG

  1. Da farko zamu wanke sausages in, sai mu tsofa su cikin tsinken tsiren mu.
  2. A cikin kwanu mai tsafta zamu zuba tangaddaden  flawan mu kofi daya, gishiri dan kadan,siga rabin kofi,cornflawa cokali biyu,bakar hoda karamin cokali daya, sai mu juya domin su hadde.                                                       
  3. Daga nan sai mu sa kwai guda daya da madara kofi daya sai a juya har zai kwabin ya haddu kamar kwabin fanke, ana son kwabin yayyi kauri.
  4. Sai mu juye kwabin a cikin kofi mai  dan zurfi domin muji daddin rufe sausage in mu da kwabin.                                                                           
  5. Zamu daura man mu a wuta yayyi zafi, sai mu saka sausauge in mu a flawa sai mu sa shi a cikin kwabin flawan mu da muka sa a kofin , mu tabbatar cewa kwabin ya rufe sausage in.
  6. Sai mu sa shi a cikin man mu da yayyi zafi, mu nayi muna juyawa har sai ya soyu da kyau .
  7. Idan yayyi brown toh corn dog in mu ya haddu, sai a sauke a ci lafiya.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho