Yadda Ake Hadda Milkshake In Strawberry Da Dabino    

0
183
Iyayan itacen strawberry da kuma dabino suna da matukar amfani da muhimmanci ga lafiyar jikin mutum.
Shi Dabino na da tsohon tarihin da wasu ‘ya’yan bishiyan ba su da shi, ba wai yanzu ba ko tun da can mutane sukan dauke shi a matsayin abinci, za kuma a iya cewa yana gaban duk wani dan itace, masamman sabo da sukarin da ya tattara a cikinsa, wannan zakin ya shafi busasshe da danye wanda ya nuna. Haka ma hukumar kula lafiya ta Amurka ta bayar da shawara ga matasa da cewa, wanda ya ke cin dabino zai sami duk abin da ya ke bukata na Magnesium, Manganese, Copper, zai sami kusan abin da yake bukata na rabin sinadaran Potassium da calcium.
Iyyen itacen strawberry kuma yana tattare da sinadarai dake taimakawa zuciya da tsarin jinni a jiki, yana karfafa hakora da kasusuwa, yana gyara fata da rage tsufa a fata, yana kuma tattare da bitamin c mai yawa wadda ke karfafa garkuwan jiki.
Abubuwan  bukata sune:
·      Dabino
·      Strawberry
·      Madara
·      Kankara
 Yadda Ake Hadda Milkshake In Strawberry Da Dabino
1.    Da farko zamu jika dabinon mu idan har abun nikanmu[blender] ba mai karfi bane amma idan yana da karfi ba sai mun jika ba.
2.    Zamu zuba jikakken dabinon mu da strawberry da kankara da madara acikin blender, zamu iya amfani da madaran ruwa ko mu samu madaran gari mu kada da ruwa mu zuba sai mu nikasu tare.
3.    Mun kamala milkshake in mu na strawberry da dabino. Sai mu zuba akofi musha shi da sanyin shi.
Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here