Zargin Shaye-Shaye Da Ake Yin Mu Ina Ganin Shi A Matsayin Babban Rashin Fahimta Da Mutane Ke Yin Mun – Inji Hamisu Breaker

0
517

Fitaccen mawakin hausa hamisu breaker, ya bayyana rashin jin dadinsa game da zargin shaye-shaye da ake yin masa, a wata hira da BBC HAUSA  tayi dashi, inda ya amsa tambayoyin da suka shafi rayuwarsa.

Mawakin ya bayyana cewa baban abun da yake kallo a matsayin rashin fahimta da mutane ke yin masa shine, Kalmar shaye-shaye da ake daura masa.

Hamisu breaker ya bayyana cewa a nashi fahimta idan har ka tasa shaye-shaye a gaba toh, bazaka cimma nasarrar ka ba.

Da aka yi mai tambaya akan meyasa mutane suke yin masa zaton? Shahararren mawakin yace ana kawo masa kyautar kayan shaye-shaye da zummar burgeshi amma kuma abune da bai damu dashi ba, ya kara da cewa Allah ya halarci mutane da dama a duniya, akwai mutani dake da siffar masu shan hayaki amma basa shaye-shaye halitta ne kawai.

Ya ce bayyan ya tsunduma waka mutani sai suka kanga masa shaye-shaye, wadda shi yake gannin idan har yayyi shaye-shaye haukacewa zaiyyi domin tunanninsa yanzu shine yadda zai farantawa masoyansa.

Rubutawa: Firdausi Musa Dantsoho