Yadda  zaku tsaftace kunnuwanku da kyau – a cewar likita

0
23

 

Bai kamata ku tsaftace kunnuwanku kwata  -kwata ba, kuma musamman ba tare da auduga cotton bud ba.

Dattin Kunnen  yana da amfani kuma yakamata jikinku ya kawar da dattin  kuni idan yayyi  yawa ba tare da sa hannun ku ba.

Dokta Lee ya yi bayani: “Earwax hade ne na sebum – wani abu mai maiko da aka samo daga sinadarin sebaceous a cikin fata wanda ke rufe ramin kunne – da matattun sel fata wadanda ke ratsawa a wannan yankin.

“Dattin kunne yana da amfani saboda, tare da  gashi da ke cikin kunne, yana taimakawa hana ƙwayoyin cuta kamar bakteriya da ƙwayoyin cutan virus shiga cikin kunnen da haifar da  cutar kunni.

“Dattin kunne a zahiri yana  zubowa daga kunnuwan ku ba tare da kun sani ba.

“Yayyin da kuke magana, ku ci ko kuma  tauna abu, tsokokin kumatunku suna tausa  hankali , kuma a ƙarshe Dattin kunin ya  faɗi da sauƙi.

” ƙaramin adadin dattin na fadowa ne lokacin da muke wanka.”

 

By: Firdausi Musa Dantsoho

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here