Sau dayawa mata da dama suna fama da larura na gyaran gashi musamman idan sanyi yazo, kama daga masu gashi mai tsayi,marasa tsayi masu shafa man retouching dama wadanda suka bar nasu natural din duk sun kasance a lokacin sanyi koda yaushe zakaji suna korafin zubewan gashi. Gashi a koda yaushe yana bukatar kulawa da kuma gyara akai- akai, haka komin karancinsa anaso ya zama yana samun kulawa sosai ba wai don kinga ai bashida yawa ya zaman kin watsar dashi sai lokacin da kikaga daman wankewa ki wankeshi ba, A’a ya zama yadda kike kula da duk wani sashi na jikinki haka shima zakina kula dashi. Toh ta nan ne zai kara yawa da kuma kyau.
Kula da gashi a lokacin sanyi wajibi ne domin idan bakayi hankali ba duk sai ya kade, saboda haka ne yau na kawo muku hanyoyin da zamubi wajen kula da gashi namu.
1) Abu na farko shi ne magance amosanin kai: Amosanin kai wadda a kafi sani da (dandruff) a turance ya kasance abu mafi illa wajen lalata gashi, domin duk yadda ka kai ga kula da gashi in har akwai amosani to zai nuna a saman gashinka, don haka ne ya kasance wajibi ki nemi magani da zai kashe miki a take. Zaki iya amfani da kanwa wajen maganin amosanin kai. wadda zaki jika kanwa da ruwa mai yawa sai ki wanke kan dashi tare da dirje duk inda akwai amosanin da yardan Allah zasu tafi.
2) Abu na biyu shi ne yawan kitso a koda yaushe: yayin da iska ya fara yawaita, gashi baya son sanyi domin idan sanyi na shiganshi toh ya samu hanyan da zai yita fita yana karyewa kenan, don haka ne ya zama dole in har baki so gashinki ya kade kiyita kitso a kai kai kuma kitso ya kasance manya ba kanana ba domin yin kitso kanan a lokacin sanyi yana kara karya gashi.
3) Steaming: steaming yana kara sanya gashi karko da kuma hanashi karyewa domin gashi a koda yaushe yana son dumi. Don haka ya kasance kina yin steaming a kalla sau daya a mako biyu.
4) Yawan oiling wato shafa mishi mai sosai: oiling gashi a lokacin sanyi yana kara taimakawa wajen hanashi karyewa domin man da zaki shafa musamman man kadanya yana taimakawa sosai wajen hana gashi karyewa.
5) Yin bayi a kalla sau daya a mako: Wasu zasuyi mamaki da nace ana yima gashi bayi, toh idan kun fahimta itama ai gashi tsirowa take Kaman fulawa, don haka idan har kinaso gashinki ta yawaita tsirowa toh ki tabbata kina mata bayi da ruwa. Bayi da ruwa ba yana nufin ki je ki sawa kanki ruwa direct da yawa ba A’a yana nufin ki samu dan wani kwalba haka wadda zaki dura ruwa mai tsafta a ciki kullum kina fesawa gashinki, idan har kina haka toh ke da ganin karyewan gashi sai dai labara.
6) Abu na karshe shine fesa turare: kamshi a gashi abu ne mai kyau musamman ga mata masu aure, domin abun kunya ne ki gama feshe jiki da turare kizo aji kai na tsami. Akwai turaruka da dama wanda akayi su musamman don gashi idan kina shafawa shima zai kara fito miki da kyan gashinki.
BY: UMMU KHULTHUM ABDULKADIR