Jami’ar Jihar Filato (PLASU) ta ce jami’an tsaronta sun dakile wani hari da ‘yan bindiga suka kai harabar jami’ar a daren ranar Talata.
Hukumar makarantar ta ce wasu ‘yan bindiga sun kai farmaki gidan kwanan daliban makarantar da ke Bokkos tsakanin daren Talata zuwa Laraba amma ba a yi garkuwa da su ba.
Mista John Agams, jami’in hulda da jama’a na cibiyar ya tabbatar wa kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN faruwar lamarin.
Agams ya ce yan bindigan sun kai hari makarantar ne domin yin garkuwa da dalibai amma jami’an tsaron dake cikin jami’ar sun dakile su.
“Gaskiya ne ‘yan bindiga sun yi yunkurin sace wasu dalibanmu, amma jami’an tsaron mu na yankin sun dakile yunkurin.
“Dalibi daya ne ya samu rauni, amma babu wani dalibi da aka sace.
“Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Benard Matur, ya shiga makarantar kuma yayi kira ga dalibai da su kasance masu zaman lafiya,” in ji shi.
Sai dai har yanzu rundunar ‘yan sandan jihar ba ta ce uffan ba.(NAN)
Firdausi Musa Dantsoho