Wata Jam’iyya Ta Janye Koken Ta kan Kalubalantar Nasaran Tinubu

0
21

 

Jam’iyyar Action Peoples Party (APP) ta gabatar da bukatar janye karar da ta shigar tana kalubalantar nasarar zababben shugaban kasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, a babban zaben 2023.

Lauyan jam’iyyar, Obed Agu, ya kuma bukaci kotun da ta yi watsi da karar.

Lauyan Tinubu, Wole Olanipekun, ya ce ba sa adawa da bukatar janye koken kuma ba su neman su biya.

Daga nan ne shugaban kwamitin mai shari’a Haruna Tsammani ya yi watsi da karar ba tare da biyan wasu kudade ba.

Jam’iyyar APP dai tana kalubalantar zaben shugaban kasa ne bisa zargin rashin bin dokokin zabe da kuma ka’idojin INEC.

Bayan korar da karar da aka yi, kotun ta tashi kuma za ta sake zama da karfe 2 na rana domin karar jam’iyyar Labour.

Firdausi Musa Dantsoho