Buhari zai dawo kwanaki kafin a mika mulki a ranar 29 ga Mayu; Likitan hakori na Landan ne ke jinkirta shi: inji Fadar Shugaban kasa

0
53

 

Shugaban kasa Muhammadu Buhari zai kasance a birnin Landan na tsawon mako guda bisa umarnin likitan hakori wanda ya fara duba sa.

Shugaban zai dawo ne, kwanaki kadan a rantsar da zababben shugaban kasa Bola Tinubu. Shugaban kasar mai ci zai mika ragamar mulki a ranar 29 ga watan Mayu.

Tun ranar 3 ga watan Mayu ne shugaba Buhari ya fice daga kasar.

Mai taimaka wa shugaban kasa kan harkokin yada labarai Femi Adesina ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa a ranar Talata.

Sanarwar ta ce “Kwararren likitan ya bukaci ganin shugaban kasar nan da kwanaki biyar don gudanar da wani aiki da aka riga aka fara,” in ji sanarwar.

Shugaba Buhari ya bi sahun sauran shugabannin duniya domin halartar bikin nadin sarautar Sarki Charles na Uku a ranar Asabar.

Wannan nadin dai shi ne na baya-bayan nan a ziyarar da ya kai kasar waje tun bayan rantsar da Buhari a matsayin shugaban kasa a shekarar 2015.

A cikin 2016, Buhari ya tafi hutun jinya na kwanaki shida zuwa Landan sannan ya tafi hutun kwanaki 10 don jinyar “cutar kunne mai ci”. A shekarar 2017, ya tafi hutun jinya a Landan, inda ya rubuta wa majalisar dokokin kasar, inda ya bukaci ‘yan majalisar su kara masa hutu.

A watan Mayun 2017, ya sake yin tafiya zuwa Landan kuma ya dawo bayan kwanaki 104.

A cikin 2018, ya sake yin tafiya zuwa Landan don wani “bita na likita,” kuma a cikin 2019, ya tafi ziyarar sirri ta kwanaki 10 a London. Ya kuma tafi Burtaniya don “duba lafiyar jiki” a cikin 2021.

Firdausi Musa Dantsoho