Yan bindiga sun kai hari kan jirgin kasar da ya taso daga Abuja zuwa kaduna a daren litinin.

0
56

Fasinjoji da dama sun jikkata yayin da wasu da dama aka ce maharan sun yi garkuwa da su.

Ko da yake hukumar ‘yan sanda ba ta tabbatar da harin ba, An tattaro cewa lamarin ya faru ne a daren ranar Litinin yayin da jirgin ya taso daga Abuja zuwa kaduna.

Rahotanni sun ce ‘yan bindigar sun kai hari kan jirgin da ke kewayen Dutse a Kaduna, mai tazarar kilomita kadan zuwa tashar jirgin Rigasa da ke karamar hukumar Igabi a jihar.

Daya daga cikin fasinjojin da ke cikin jirgin ya ce ‘yan bindigar sun yi wa kan titin jirgin ruwan bama-bamai da wata na’urar fashewar bama-bamai (IED), lamarin da ya tilasta wa jirgin ya kauce hanya.

Bayan da jirgin ya tsaya, an ce maharan sun fara harbe-harbe akai-akai.Ya kara da cewa daga baya ‘yan ta’addan sun kutsa cikin jirgin inda suka yi garkuwa da wasu mutanen da ba a tantance adadinsu ba, inda ake fargabar an kashe wasu.

A halin da ake ciki, an tattara sojoji zuwa inda harin ya faru domin ceto sauran fasinjojin.

Wani fasinja da ke cikin jirgin, Anas Danmusa, ya wallafa a shafin sa na Facebook yana kuka yana neman taimako.

A cewarsa, kusan sa’a guda babu wanda  ya kai musu dauki a cikin lamarin ,yayin da maharan suka yi kokarin shiga cikin jirgin da karfi.

Bayan kimanin mintuna 20, Danmusa ya tabbatar da cewa jami’an soji sun isa wurin kuma sun kawo musu dauki.

By Fatima Abubakar