Gwamnatin Jihar kano ta magantu kan Ayyukan Hisba a jihar.

0
54

Gwamnatin Jihar kano ta magantu kan Ayyukan Hisba a jihar

 

 

 

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf, ya gargadi Hukumar Hisbah ta jihar da ta rika taka-tsan-tsan wajen kiyaye hakkin dan Adam a yayin aiwatar da ayyukanta.

Gwamnan ya yi wannan kiran ne a wani ɓangare na jawaban da ya gabatar yayin ganawa da malamai a Fadar Gwamnatin jihar Kano.

Gwamnan ya kuma bayyana damuwarsa kan wani bidiyo da ya ce ya yi arba da shi, kan yadda Hukumar Hisbah ta jihar ke gudanar da ayyukanta wajen kama wadanda ake zargi da aikata laifuka masu nasaba da bata tarbiyya

Sai dai Kuma a yayin taron Abba Gida-Gida ya yi wa malamai nasihar lura da nauyin da rataya a wuyansu, in da cewa ya ga wani bidiyon jami’an Hisbah suna cicciba ‘yan mata da samari ana dorawa a mota da sunan ana kamasu Wanda hakan ba daidai bane, kamata yayi mata su kamo mata cikin mutunci da mutunta dan Adam suma jami an maza suyi hakan.

Inda a  cewar sa, “Hisbah Hukuma ce mai albarka wadda muka dauka da martaba, kuma muka ɗauko bayin Allah wadanda  muka san za su iya, muka ce ga amanar al’ummar Jihar Kano.

Kuma  “A mahangar Hukuma shi ne ta yi abin da ya ke daidai, kuma ta bai wa Gwamnatin shawara sannan a samu hadin kai tsakanin Gwamnati da masu ruwa da tsaki”

Wannan bidiyo da ya tayar min da hankali, shiyasa nake kira da jan hankali don gyara muke so.

“An ɗebi motoci, an je inda wasu matasa ke ɓarna maza da mata, amma yadda aka riƙa debo su ana duka da gora, suna gudu ana bi, ana tadile kafafunsu, ana debo su kamar awaki haka a jefa su a cikin Hilux Bai kamata ba”

 

Sai dai ya Kara da céwa “Alhalin Wani in kashin bayansa wato Spinal Cord ya karye ya gama yawo kenan har abada, Allah ma ya kiyaye, wannan muna ganin kuskure ne babba, ka rungumo matashiya ko matashi kuna jefa shi kamar akuya a cikin Hilux sam abin babu dadi.

Sannan naga bidiyon da aka je inda ɗaliba a Jami’ar Bayero suke ma ana har inda suke,wato dakunansu ana duka ana rungumosu, ana jefa su a cikin mota.

Mu muna ganin akwai gyara. Mun saka hukuma saboda ta yi wa addini musulunci hidima, amma idan anayin  irin wannan to yaran ma sai su kangare, a maimakon suyi abin da ake so su yi na gyaran sai a samu akasin haka. Allah Ya kiyaye.

 

Idan yaran nan suka kangare mana a Jihar Kano, yaya za mu yi da su? Amma a fita da motoci, a fita da jami’an tsaro, a hada da Hisbah, a hada da ‘yan sanda, a hada da civil defence, amma ba ma so a hada da sojoji, don idan aka hada da su to abin ya girma kenan.

Mun yar je a tafi da Yan sandan farin kaya , duk inda aka san ana wannan aiki marar kyau, a je a kamo wadannan yara ko wadannan mutane a danka su a hannnun hukuma, don Allah Yana son ka kare mutuncin dan Adam Kuma ka dauke shi dan uwanka,” inji Gwamnan.

Daga karshe yayiwa Hukumar dama jihar kano da kasar Baki daya adduar dorewar zaman Lafiya.

 

 

 

Hafsat Ibrahim