Yan uwan wayanda aka yi garkuwa da su a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna sun yi tattaki zuwa ofishin sufuri na jirgin kasa a yau litinin.

0
95
smart

Iyalan wadanda jirgin kasan ya rutsa da su sun yi tattaki zuwa ma’aikatar sufuri a ranar Litinin don nuna rashin amincewarsu da ci gaba da zaman ‘yan uwansu a cikin kogon ‘yan ta’adda.

Hakan ya biyo bayan wani faifan bidiyo da ‘yan ta’addan suka fitar inda ake yi wa mazajen da aka kama bulala ba tare da tausayi ba.

Iyalan da suka kasance a ma’aikatar tun karfe shida na safe, sun ce sun je ne domin nuna bacin ransu kan ci gaba da zaman wadanda ake tsare da su.

Sun sha alwashin ba za su tafi ba har sai an tabbatar musu da dawowar ‘yan uwansu.

Za mu ci gaba da kawo muku sabbin karin cikakkun bayanai daga baya yayin da suka shigo.

Daga Fatima Abubakar