Shin kun san cewa yayan gwanda suma suna da amfani sosai ga masu fama da ciwon sukari? Ga duk abin da kuke buƙatar sani game da hakan.
Ciwon sukari yanayin rayuwa ne wanda miliyoyin mutane a duniya ke rayuwa dashi. Cuta ce, da ke da alaƙa da hauhawar matakan sukari na jini da ƙarancin matakan samar da insulin. Abu mai kyau shi ne cewa tare da daidaitaccen nau’in abinci da canje-canjen salon rayuwa, ana iya sarrafa ciwon sukari cikin sauƙi. Akwai wasu abinci, hatsi da kayan masarufi waɗanda za’a iya ƙarawa cikin abinci don daidaita matakan sukarin jini yadda yakamata. Masana abinci sun kuma ba da shawarar wasu ‘ya’yan itatuwa da masu ciwon sukari za su iya sa su cikin amincin su, kuma ɗaya daga cikinsu shine gwanda. Shin kun san cewa yayan gwanda suma suna da amfani sosai ga masu fama da ciwon sukari? Anan ga duk abin da kuke buƙatar sani game da fa’idodi, illolin da kuma yadda ake amfani da yayan gwanda a abincin masu ciwon sukari.
Gwanda yana da wadatar fiber mai yawa, shi ya sa masana ke ba da shawarar a ci shi a abincin masu ciwon sukari. Hakanan yana kiyaye tsarin narkewar abinci lafiya kuma cikin tsari mai kyau. Tunda abinci ne mai matsakaicin GI, baya haifar da hauhawar sukari a cikin jini. Bincike ya gano cewa gwanda yana da amfani ga masu ciwon sukari – ba kawai ‘ya’yan itace ba, har ma da iri.
An ce yayan gwanda na da matukar amfani ga masu ciwon sukari. Sinadarin papain enzyme wadda ke cikin gwanda yana taimakawa wajan narkar da abinci kuma akwai wasu fa’idodi da yawa na cin ‘ya’yan gwanda a kowace rana.
Ga wasu faidar sa:
1. Kamar gwanda, hatta yayan gwanda na da wadataccen fiber. Wannan ya sa su ka dace don kiyaye lafiyar zuciya da kuma daidaita ciwon sukari.
2. Har ila yau, yayan gwanda na da polyphenols, flavonoids da sauran masu yawa a cikin sa waenda ke iya ba da kariya daga cututtuka masu tsanani kamar ciwon sukari.
3. Wani bincike ya gano cewa yayan gwanda yana hana masu ciwon sukari tsananin damuwa.
4. Bincike ya ba da shawarar cewa yayan gwanda kuma na iya taimakawa wajen rage sukarin jini kai tsaye saboda sinadarin rigakafin ciwon sukari da ke cikinsu kamar methyl ester, hexadeconic acid da oleic acid.
Yayan gwanda ba su da haɗari idan aka ci, amma ya kamata a ci su matsakaici. Dole ne a lura da wasu abubuwa guda biyu game da illolinsu kafin cin su.
1. Ya’yan gwanda suna da ɗaci sosai, shi ya sa za su iya haifar da wani irin matsala na hanji ga wasu mutane.
2: Masana sun lura cewa mata masu juna biyu ko masu shayarwa yakamata su guji cin yayan gwanda da yawa, domin enzymes din cikinsa na iya yin illa ga jikin su.
Tunda yayan gwanda na da ɗaci sosai, yana da wuya a cisa danye. Kuna iya mai da shi foda ku rika sawa a ruwan ‘ya’yan itace, smoothie , ko a saman kayan zaki.
Ku tabbatar da cewa ba ku wuce gona da iri ba wajan amfani da yayan gwanda , kuma ko da yaushe ku tuntuɓi likita ko masanin abinci mai gina jiki kafin yin wasu manyan canje-canje a cikin abinci ku.
Daga: Firdausi Musa Dantsoho