Zababben Shugaban Kasa, Tinubu Ya Tashi Daga Nijeriya Zuwa Turai A Ziyarar Aiki

0
34

Zababben shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a ranar Laraba da yamma ya bar Najeriya zuwa Turai domin ziyarar aiki.

Zai yi amfani da damar tafiya don daidaita tsare-tsare da shirye-shiryen mika mulki, da zabin manufofinsa tare da wasu manyan mataimakansa ba tare da matsananciyar wahala da damuwa ba.

A yayin ziyarar, zababben shugaban kasar zai tattauna da masu zuba jari da sauran manyan abokan hulda da nufin tallata guraben zuba jari a kasar da kuma shirye-shiryen gwamnatinsa na samar da yanayi mai kyau na kasuwanci ta hanyar manufofi da ka’idoji.

Tuni, an jera tarurruka tare da ‘yan kasuwa daga bangarori daban daban a cikin kasuwancin Turai da suka hada da masana’antu, noma, fasaha da makamashi.

Asiwaju Tinubu na fatan gamsar da su kan shirin Najeriya na yin kasuwanci a karkashin jagorancinsa ta hanyar hadin gwiwar da za ta amfana da juna kan samar da ayyukan yi da kuma samun kwarewa.

Farfado da tattalin arzikin kasar ya zama wani babban ginshiki na ajandar Tinubu kuma taron na daya daga cikin kokarinsa na sake farfado da martabar Najeriya a tsarin tattalin arzikin duniya da samar da damammaki ga dimbin matasan kasar.

Ya zuwa yanzu dai zababben shugaban kasar ya yi alkawarin zai kai nasara kuma ziyarar na nuni da jajircewarsa kan wannan alkawari domin tuni ya fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki na duniya kan muhimman batutuwan da suka shafi tattalin arziki da tsaro.

Kafin ya bar kasar, Asiwaju Tinubu ya gana da ‘yan takarar majalisar wakilai da ‘yan takarar shugaban majalisar wakilai da mataimakinsa wanda jam’iyyarsa ta APC ta amince da su, Tajudeen Abbas da Hon. Benjamin Kalu, wanda kungiyar hadin gwiwa ta majalisar ta gabatar masa.

An shirya zai dawo nan ba da jimawa ba don shirye-shiryen rantsar da shi a hukumance a matsayin shugaban kasar na 16 a ranar 29 ga Mayu, 2023.

 

Firdausi Musa Dantsoho