Dan takarar gwamnan jihar Kaduna a karkashin jam’iyyar All Progressives Congress (APC) Uba Sani ya bayyana abokin takararsa.
A wata sanarwa da ya fitar a daren jiya Litinin, Sani ya bayyana Hadiza Balarabe a matsayin mataimakiyar ‘yar takarar gwamna.
Sani shine Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, yayin da hadiza Balarabe ke rike da mukamin mataimakin gwamna Nasir El-Rufai a halin yanzu.
Dan majalisar ya bayyana cewa matakin nasa ya biyo bayan tuntubar masu ruwa da tsaki na jihar.
Sani ya ce hadiza Balarabe ta ba da gudummawa ga “gaggarumar ci gaba da gwamnatin Mallam Nasir El-Rufai ta samu a fannin samar da ababen more rayuwa da ci gaban bil’adama”.
ya kara da cewa, hadiza ta nuna kwazon aiki, aiki a kan lokaci, sadaukarwa da hadin kai wajen sauke nauyin da aka dora mata.
Dan takarar jam’iyyar APC ya yi kira ga al’ummar Kaduna da su goyi bayan zabin su kuma zaben jam’iyyar a shekara mai zuwa.
El-Rufai dai ya goyi bayan uba Sani ya zama Sanata a shekarar 2015. Sannan ya doke Shehu Sani wanda ya wakilci Kaduna ta tsakiya a majalisar wakilai ta 8.
An yi imanin cewa gwamnan ya yi aiki ne don ganin Sani ya zama dan takarar jam’iyyar a zaben 2023.